✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aisha Buhari ta fice daga taron APC a fusace

Aisha Buhari ta fice daga taron cikin bacin rai, duk da cewa zaben fitar da gwanin shugaban kasar jam’iyyar ya gudana cikin lumana

Rahotanni daga zauren babban taron dan takarar shugaban kasar jam’iyyar APC sun nuna mai dakin shugaban kasa, Aish Buhari, ta fice daga wurin taron a cikin bacin rai.

An ga Aisha Buhari ta fice a motarta daga wurin taron ranta a bace, duk da cewa zaben fitar da gwanin shugaban kasar jam’iyyar ya gudana cikin lumana.

Aminiya ta gano cewa an yi ta kiran Aisha Buhari domin ta rako shugaban kasar kan dandamali tare da sauran shugabannin APC, amma ta ki.

Hakan ta faru ne bayan wanda ya lashe zaben fidda gwanin, tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu, ya kammala jawabinsa.

An kira Buhari zuwa kan dandamlin ne domin ya mika wa Tinubu tutar jam’iyyar APC a matsayin dan takara jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.

Sauran wadanda aka gayyato domin su rako Buhari sun hada da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Adamu, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da sauransu.

Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin bacin ran da ya Aisha Buhari ta fice daga wurin taron ranta a bace ba.