Sunnah ce ga namiji ya yi sassarfa a Badanul Masili. Sunnah ce ga namiji ya taka saman Safa da na Marwa don yin addu’a. Haka kuma yake Sunnah ga mace ta taka saman duwatsun nan idan wurin babu turmutsitsin mutane lokacin yin addu’a a kan Safa da Marwa.
Fadakarwa: Duk lokacin da aka tada Sallah ta farilla a Masallacin Ka’aba, to, mai yin Dawafi ko Sa’ayi, zai dakata da abin da yake ciki, don ya bi liman, ya yi koyi da shi a cikin wannan Sallar. Da mai Hajji ya kare Sa’ayi sai kuma ya koma masaukinsa, ya dakata, ya saurari zuwan ranar takwas ga Zul-Hajji. Wato ranar Tarwiyya ke nan.
Rukuni na Uku (Tsayuwa a kan Arfa)
Idan mai aikin Hajji ya isa Arfa a ranar tara ga Zul-Hajji, an so ya sauka a wani wuri da ake kira Namira. Idan rana ta karkata, sai ya yi wankan tsayuwar Arfa. Ba zai cudanyi jikinsa da karfi ba. Mace mai haila ko jinin biki za ta yi wannan wanka; domin ana yin sa ne don tsayuwar Arfa, ba don Sallah ba. Babu laifi a kan mutum idan bai yi wankan nan ba. Sa’an nan ya nufi Masallacin Namira, a nan masallacin zai yi Sallar Azahar da La’asar a hade tare da liman. Kowacensu za a sallace ta Sallar kasaru, wato a gajarce ta raka’a biyu kadai. Kowacce daya daga cikinsu za a yi mata nata kiran Sallah da tada ikama. Kowace Sallah daga cikinsu za a yi mata karatu a asirce koda kuwa sun dace da ranar Juma’a ce. Domin a Azahar za a sallace ta, ba Juma’a ba. Wadannan salloli in zai yi su ba tare da liman, sai ya yi su a hade shi kadai a nan inda ya kafa tantinsa.Dalilin yin wadannan salloli a Sallar kasaru shi ne komai kusancin garin da mutum ya fito, zai yi kasarun nan, matukar dai wurin da ake yin Sallan nan ba shi ne ainihin garinsu ba.
Bayan kare sallolin nan, Azahar da La’asar, sai mahajjaci ya je cikin filin Arafa ya tsaya. Kowane yanki na filin Arfa mutum ya tsaya a cikinsa, tsayuwar ta kasance tsakanin wasu duwatsu da ke tsakiyar Arfa kusa da Jabalur Rahmati. Mutum zai tsaya har bayan faduwar rana, kuma har dare ya dan shigo, sa’annan ya bar Arfa ya nufi Muzdalifa. Tsayuwa a kan Arfa, tun daga Azahar zuwa faduwar rana wajibi ne. Idan mutum bai yi ba, ya bar wajibi, don haka zai yi hadaya. To, amma tsayuwar nan ta tsakanin faduwar rana da fitowar alfijir, ita farilla ce, wato rukuni cikin rukunan aikin Hajji, farilla ce ga kowane mahajjaci ya zama ya samu dan lokaci komai kankantarsa da zai tsaya a kan filin Arfa, a cikin daren Babbar Sallah. Mafi karancin tsayuwar shi ne mutum ya tsaya har gabobin jikinsa su natsu da niyyar yin wannan tsayuwa. Wanda duk bai samu yin wannan tsayuwa ta dare ba, har alfijir ya rigaya fito, to, Hajjin wannan shekarar ya kubce masa ke nan. Amma fa duk a cikin mazhabobin nan na Musulunci hudu, Mazhabar Malik ce kawai ta dauki tsayuwar maraice a matsayin wajibi, tsayuwar dare kuwa a matsayin farilla. A sauran mazhabobi kuwa kowace tsayuwa ta rana ce ko ta dare ce, tana iya zama farilla, ta kuma wadatar. Sai dai dukkansu sun fi son kaiwa har bayan faduwar rana a nan Arfa.
A lokacin da mutum yake Arfa, an fi son ya dage a tsaye, ba a zaune ba. Dagewa a tsaye mustahabbi ne ga namiji kawai, ban da mace. Mustahabbi ne ya yi tsayuwar a kan dabba, kuma ya zama yana da alwalarsa. Amma idan mutum ya gaji da tsayin ko hawan dabbar ko rike alwalar, to an so ya yi akasi don ya shakata. A duk lokacin da mutum yake yin tsayuwa, ana so ya yi ta yin zikiri kamar tasbihi ko hamdala ko hailala ko salatin Annabi (SAW) ko rokon Allah ko addu’a ga iyaye. Ana son mahajjaci kada ya yi azumi a ran nan don ya ji karfin yin ibada
Kwana a Muzdalifa
Da kare tsayuwar Arfa, bayan faduwar rana, sai mahajjaci ya bar Arfa, ya nufo Muzdalifa a nan Muzdalifa zai yi Sallar Magariba da Isha’i tare da liman a hade ko shi kadai. Za a yi Sallar Isha’i kasaru, sai fa ga mutanen Muzdalifa su kadai, su kam sai sun cika ta raka hudu. A nan Muzdalifa mahajjaci zai kwana. Washegari idan alfijir ya fito, sai ya yi Sallar Asuba tare da liman a cikin Masallacin Muzdalifa ko shi kadai, bayan kare Sallar sai ya tsaya a wurin da ake kira Mash’arul Harami ya sa fuskarsa tana kallon Alkibla, ya yi ta addu’a har zuwa kusan fitowar rana. Sa’annan ya daina tsayuwar, ya bar Muzdalifa, ya nufi Mina, kwana a Muzdalifa har alfijir ya fito ranar Sallah, ba da wani uzuri ba, to zai yi hadaya sadaka idan kuwa ya bar saukar nan don wani uzuri ne to babu komai a kansa.
Sauka a Mina da Jifar Jamra (Jifar Shaidan)
Idan mahajjaci ya baro Muzdalifa, ya taso wa Mina, a ranar goma ga Zul-Hajji idan ya iso wani kwari da ake kira Badanul-Muhassir, zai yi sauri a wajen tafiya har ya wuce shi idan kuwa a kan dabba yake zai motsa ta ta yi sauri, yin wannan saurin mustahabbi ne. Da mutum ya shigo Mina ba zai sauka ko’ina ba tukuna, sai ya zarce zuwa Jamratul-Akaba, ya jefe ta da ’yan duwatsu kanana guda bakwai. Da ma zai yi tanadinsu ne tun a Muzdalifa. Ga sharuddan ingancin wannan jifar, zai kama dan dutsen nan da babbar yatsarsa da manuniyarsa a wani kauli kuwa da babbar yatsarsa da yatsarsa ta tsakiya, sa’anan ya jefa, idan bai yi haka ba jifa ta baci kuma wajibi ne ’yan duwatsun su kai adadinsu, wato tsakuwa bakwai. Idan sun kasa haka jifar ba ta yi ba, sai ya cika su. Kuma wajibi ne abin jifar ya zamo dutse ne ko tsakuwa. Ba a yin jifa da laka ko karfe. Wajibi ne girman dutsen jifar ya zama kamar kwayar gujiya (Kwaras-kwaras). Ba a jifa da dutse babba ainun ko kankane ainun.
Mustahabban jifa su ne, ya ce ‘Allahu Akbar!,’ a lokacin da yake jefa kowane dutse. Kuma jifar duwatsun nan bakwai ta zama a jere, ba dakatawa a tsakaninsu. Kuma an so duwatsun nan su zamo tsitsinto su ya yi, wato ba falale ne ya dauka ya farfasa shi ba. Kuma an so dutsen ya zama mai tsarki. Kuma kada ya zamo wanda ya rigaya ya yi jifa da shi ne da farko kuma an so ya zama daga cikin kwarin nan ya yiwo jifar. Idan mutum ya bar wadannan mustahabbai, ba abin da ya taba Hajjinsa. Lokacin jifar Jamratul Akaba shi ne tun daga fitowar Alfijir na Ranar Sallah har zuwa faduwar rana. Bayan faduwar rana jifar ta zama ramuwa. Wato ana iya rama ta da dare, ko washegari da rana.
Da mahajjaci ya kare jifar Jamratul Akaba, sai ya je ya sauka a masaukinsa na Mina. Ya yanka hadayar da ya zo da ita a nan Mina. Sa’annan ya yi aski ko saisaye idan namiji ne. Mace za ta rage gashin kanta kadan da almakashi. Idan wanda yake da ciwo ga kai ya zama ba ya iya yin aski ko saisayen, to an yafe masa yin su, amma zai yi hadaya don barin yin dayansu.
Dawaful Ifada
Bayan kare aski ko saisaye a ranar goma ga Zul-Hajji, sai mahajjaci ya nufi Makka don ya yi gewayon Dakin Ka’aba, gewayon Ifala. Ma’anar kalmar “Ifala” ita ce mutane da yawa su dungumo sai ka ce fari. Wannan gewayo ana kiranta Dawaful-Ifala, shi kuwa farilla ne. shi ne rukuni na hudu, wato na karshe, a cikin aikin Hajji. Yin sa farilla ne, idan bai samu ba Hajji ya baci. Wannan Dawafi ana yin sa daidai yadda ake yin Dawaful Kudumi, da aka yi bayaninsa a baya. Ga niyya kadai suka bambanta. A wannan zai ce: “Na yi niyyar yin Dawaful Ifala farilla. Wancan kuwa Dawaful-Kudumi, wajibi. Kuma shi wannan Dawafi babu sassarfa a cikinsa. Bayan mahajjaci ya kare gewayon Daki sau bakwai, zai yi Sallah raka’a biyu a Makamu Ibrahim.
Idan mahajjaci ya kare dawafinsa a Ranar Sallah, sai ya kai yammaci sai ya koma Mina, ya kwana uku, don jifar Jamrar Shaidanun nan guda uku. A ranar 11, 12 da 13 na Zul-Hajji, kullum zai je ya jefi dukkan jamrorin nan uku, kowanne da dutse bakwai bayan rana ta gushe daga tsakiya, kafin ya yi Sallar Azahar. Zai yi jifar nan kamar yadda aka siffanta a baya. Zai fara da jifar Jamratul Ula sau bakwai, ya tsaya ya yi addu’a sa’annan ya zarce Jamratul Akaba ita ma ya jefe ta sau bakwai, amma ba zai tsaya yin addu’a a bayanta ba.
*****
Lokacin yin wadannan jefe-jefe shi ne daga gushewar rana daga tsakiya har zuwa faduwar rana lokacin ramuwar yin jifa shi ne dare ko yini na kashegari. Lokacin yin jifa yana karewa da faduwar rana na yinin goma sha uku ga ZulHajji. Bayan wannan lokaci jifa ta kubce sai yin hadaya. Idan mutum ya bar yin jifa dungum, zai yi hadaya. Wanda ya ke cikin gaggawa an yafe masa jifa ta ranar karshe.
DAWAFIL WADA’I NA BAN KWANA
Wajibine a gare shi, a ranar da zai bar Makka ya je Masallacin Ka’aba ya yi gewayon daki sau bakwa, domin yin Sallama da Ka’aba. Wannan dawafi ana kiransa Dawaful Wada’i watau na bankwana. Shi kuma Wajibi ne.