HUKUNCIN HAJJI
Tun farko dai ya kamata mu san shin mene ne Hajji? To Hajji wata Ibada ce wadda ta tara Ihrami (Niyya) da Dawafi (kewayon dakin Ka’aba) da Sa’ayi (Tafiya tsakanin safa da marwa) kuma da tsayuwa a kan Arfa da sauransu. Hukuncin yin Hajji farilla ne a kan mumini da mumina su aikata shi sau daya tak a cikin rayuwarsu ta duniya. Kuma Sunnah ne ga mutum ya maimaita yinsa a kowace shekara idan ya samu halin. Yin Hajji yana daya daga cikin shika-shikan Musuluncin nan guda biyar. Su ne Kalmar Shahada, Sallah, Azumin Watan Ramadana, Fidda Zakka, da Hajjin Dakin Allah mai alfarma ga wanda ya samu iko. Ma’anar kalma Hajji ita ce ziyara.
Hajji ba ta zama wajibi a kan mutum sai sharudda biyar sun samu gare shi tukunna ga su:
- Zaman ‘Yanci: Hajji ba ta wajaba ba a kan bawa, ko baiwa. Amma idan sun aikata shi ya zama na nafila. Saboda haka za su sake yin wani aikin Hajjin na farilla a lokacin da suka sami zama ‘yantattu.
- Balaga: Hajji ba ta wajaba ba a kan yaro ko yarinya wadanda bas u balaga ba. Idan yaro ko yarinya, ko bawa ko baiwa, suka yi Hajji to Hajjinsu daidai ne kuma za su sami lada. Sai dai wannan Hajjin nasu ba zai wadatar da su ba daga yin Hajjin Farilla a lokacin da yaro ko yarinya suka balaga, ko kuwa bawa ko baiwa suka ‘yantu da su sake yin na farilla.
- Hankali: Hajji ba ta wajaba ba a kan Mahaukaci.
- Musulunci: Hajji ba ta wajaba ba a kan kafiri, kuma ko ya yi ba ta inganta ba.
- Samun Ikon Zuwa Hajji: Abin da ake nufi da samun ikon shi ne, na farko zamantowar hanya lafiyayye, amintacce. Idan mutum yaji tsoro a kan wani abu zai same shi ko kuwa zai taba dukiyarsa ta hanyar zalunci, to Hajji ta fadi daga kansa. Sai dai shi zalumci a kan dukiya ba zai hana aikin Hajji ba sai idan yawan abin da za a karba ya isa ya cuci iran wannan mutumin. Abu na biyu game da ma’anar samun ikon zuwa Hajji shi ne samun guzuri da zai kai mutun Makka ya kuma maido shi gida. Na uku shi ne mutum ya zama yana da karfin jiki na lafiya Makka da wuraren aikin Ibada na Hajji, ko a kan kafafunsa ko a kan dabba. Abu na hudu shi ne samun lafiyar jiki a kan tafiya. Don haka Hajji ya fadi a kan marasa lafiya Amma makanta ba za ta hana zuwa Hajji ba idan makahon zai iya samun wanda zai kai shi.
FADAKARWA.
Kalmar Farilla ko wajibi ma’anarsu daya ce a cikin dukan ayyukan Ibada, ban da Hajji, a cikin Babin Hajji akwai bambanci tsakanin Farilla da wajibi. Farilla a cikin Hajji, ita ce abin da zai sa Hajji ya baci domin barinsa. Wajibi kuwa shi ne wani aiki muhimmi a cikin Hajji wanda idan mutum ya bar shi ya yi laifi. Amma laifin bai isa ya bata masa Hajjinsa ba, sai dai zai gyara laifinsa ta hanyar yin hadaya, sadaka, ko yin fidiya sadaka, ko kuwa ba da tafi daya na abinci sadaka idan laifin kankane ne. To zai gyara laifin nan ta hanyar yin sadaka da wata dabba ta gida don sakamakon wata dabba ta daji da ya kashe. Zan sake yin magana a kan wadannan abubuwa filla- filla a nan gaba.
Yanzu mun san cewa kalma farilla a cikin babin Hajji ita ce abin da Hajji zai baci sosai idan ba a aikata shi ba. To duk abin da ya ke farilla a cikin aikin Hajji abu hudu ne kawai.
FARILLAN HAJJI
- Ihrami, watau kudurta niyyar yin Hajji a cikin zuciya.
- Dawaful-Ifada, watau gewaya Dakin Ka’aba sau bakwai.
- Sa’ayi watau tafiya tsakanin safa da marwa sau bakwai.
- Tsayuwa a kan filin Arfa a daren Babbar Sallah a wata mazhabar kuwa wadda ba ta Malikiyya ba tsayuwa a kan Arfa da yamma, da rana a ranar tara ga Zulhaji ta isa.
Wadannan su ne farillan Hajji guda hudu, da wani suna kuma ana kiransu rukunnan aikin Hajji. Nan gaba zan yi Magana a kan ko wannensu da cikakken bayani.
Za mu ci gaba