✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Aikin gidauniyarmu tallafa wa gajiyayyu da mabukata’

Aminiya ta tattauna da Shugaban gidauniyar Tallafa wa Mabukata da ke Kano, Malam Auwal Muhammad danlarabawa, inda ya yi bayani game da yadda suke tallafa…

Aminiya ta tattauna da Shugaban gidauniyar Tallafa wa Mabukata da ke Kano, Malam Auwal Muhammad danlarabawa, inda ya yi bayani game da yadda suke tallafa wa gajiyayyu, marayu da sauran mabukata da ke cikin al’umma:

Aminiya: Ko za ka yi bayanin a takaice game da gidauniyarku kuma tun yaushe aka kafa ta?

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, wanda ya bamu damar kasancewa cikin koshin lafiya da kuma kasancewa cikin wannan aiki na tallafa wa mabukata ba tare da gajiyawa ba. Allah Ya kara mana imani da ikon yin ayyukan alheri a rayuwarmu har mu koma ga Allah (swt), mu rayu muna Musulmi, sannan mu koma gare shi muna Musulmi.
Gidauniyar Tallafa Wa Mabukata, ta samu sunanta ne daga tunanin Auwal Muhammad danlarabawa, daga nan ta zama an kafa ta a ranar 1 ga Janairu, 2011. Tare da wasu mutane uku, aka ci gaba gudanar da harkokin gidauniyar har ta kai ga kananan hukumomi har zuwa wasu jihohin kasar na. Mun samar mata da iyaye da kwamitin amintattu da kuma na gudanarwa. Sannan muka yi rijistarta da wasu hukumomi da suka wajaba bisa doka.
Aminiya: Mene ne manufar gidauniyar?
Manufar kafa wannan gidauniya shi ne don a samu wata kafa da za ta rika tallafa wa al’ummarmu, kama daga marayu, tsofaffi, matasa, yara, nakasassu da marasa lafiya, wanda a cikin manufar ce muka samar da tsarin tallafa wa marasa Lafiya da basu da ikon biyan kudin da za a yi masu aiki a asibiti, sannan muka samar da tsarin tallafa wa marayu da koya musu sana’o’in hannu, muka samar da tsarin ba da gudunmawar tallafin karatu. Muna samar da tsarin fadakarwa da wayar da kai wajen kiwon lafiya, tsaftace ruwan sha da gina burtsatse da gyara makabartu da bada likkafani kyauta.
Aminiya: Ta yaya kuke samun kudin shiga kuma ta yaya mabukata za su ci gajiyar tallafin gidauniyar?
Gidauniyar Tallafa Wa Mabukata tana da tsari na samar da kudin shiga. Da farko a junanmu muke hada kudi mu kai ziyara gidan marayu da asibitoci. Daga baya muka bude mata shafuka a zaurukan sada zumunci na Facebook da Twitter, inda muka. Daga nan sai muka fara samun masu ba mu gudunmawa don ci gaba da tallafa wa mabukata. Cikin nasara abu kullum kara karbuwa yake ga masu son tallafa wa mabukata. Muna neman kuma kanfanoni, mawadata, sarakai, malamai, gwamnati da kungiyoyi su kara tallafa wa wannan gidauniyar, don samun ci gaba da wannan ayyuka na tallafa wa mabukata.
Mabukata suna samun gajiyar tallafin da ake samu ta hanyar kundin masu neman tallafi da muke da shi, wanda kodayaushe mabukata na zuwa ofishinmu da ke lamba 116, Kwanar Jaba, kan titin PRP a Kano, kusa da gidan Mai Unguwa don neman tallafi. Sannan mukan bibiyi mabukata da kuma sanin gidajen da suke har, ma mukan kai masu son tallafawa su je su gani da idanunsu kuma su tallafa musu kai tsaye. Muna shiga birni da karkara don duba yadda rayuwa take kasancewa, don samar da tallafi a gare su.
Aminiya: Ko za ka ba mu misalin wasu ayyuka da gidauniyar ta gudanar a baya?
Gidauniyar nan ta yi ayyukan alheri da dama, wadanda suka hada da kira ga gwamnati da ta taimaka wa wadanda gidajensu suka rushe, sakamakon ruwan sama kuma aka tallafa musu, muka je da wadanda ba su da damar daukar tallafin muka dauka aka kai musu har gidajensu. Ta yi aikin gina burtsatse a unguwar PRP kuma mun koyar da marayu mata sana’o’in hannu kyauta. Ta raba wa mabukata rancen kudi yin sanaa ba tare da kudin ruwa ba, karkashin tsarin Rumbu Collection daga Muhammad Bello Sani. Sannan da azumi mun yi ciyarwa kuma mun samu wata baiwar Allah da ta raba wa marayu da mabukata kimanin su 1000, Naira dubu 10 kowannensu. Wasu kuma mutum kimanin 500 suka samu Naira dubu biyar-biyar. A bikin Sallah kuma akan yanka shanu don a raba wa marayu su ma, su samu damar yin Sallah cikin walwala da annushuwa. Kana mukan raba sutura ga marayu da mabukata da almajirai ko tabarmi da butar alwala ga masallatai. Ta koya wa mata yadda ake karbar haihuwa kyauta, tare da ba su kayan aiki na zamani. Ta gyara gidajen marayu da mabukata wanda ruwa ya rusa har kimanin 65. Akwai kwamitin wayar da kai wajen cututtukan zamani, da kwamitin fadakarwa da suke shiga makarantu da unguwanni don gyaran zukata da zamantakewa da tsafta. Haka mun dinka wa yara ’yan makaranta yunifom da littattafai don su koma makaranta. Ta sama wa marasa lafiya tallafin kudin da za a yi musu aiki a asibiti da dama da sayen magani. Sannan ta bude ofishinta a cikin unguwar da take da yawan al’umma mabukata, don samun bayanai da kuma yadda za a musu.
Aminiya: A matsayinka na shugaban wannan gidauniya, wane kira za ka yi ga al’umma?
Kiran da zan yi ga dukkan masu tallafawa shi ne, al’ummarmu na cikin wani hali mai muni, wanda ba kowa ne ya san da hakan ba sai an kai shi ya gani da idanunsa zai tausaya. Wasu ma idan muka kai su har kuka suke yi don tausayi. Abin da za a ci a gida yana wahala, maganin day a kai Naira 1000 sai dai su hakura su koma gida, ga yawan barace-barace, wajen kwanan wasu idan aka je aka gani ba za a dauka dan Adam ne a cikinsa ba. Da abubuwa da dama na tausayawa, don haka muke kira ga al’umma da su tallafa iya kokarinsu.