Kimanin shekara takwas ke nan da fara aikin asibitin masu cutar daji “International Cancer Center” da ke kusa da unguwannin Chika da Alaita a titin zuwa filin jirgin sama na Abuja, inda yanzu aikin ya tsaya.
Matar marigayi Shugaban kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa ta kafa asibitin bayan kaddamar da wata gidauniya a watan Yulin shekarar 2009 inda aka yi kudirin tara Naira biliyan 10 domin gini da sanya na’urori da sauran kayan aiki a asibitin. Sai dai babu wanda zai iya cewa ga takamaiman abin da aka tara a bikin.
Hajiya Turai ’Yar’aduwa ta fadi a wurin kaddamar da gidauniyar cewa ta yi burin tallafa wa masu cutar daji musamman matalauta, domin ’yan Najeriya da dama suna fama da cutar. Ta ce ta yi wannan yunkuri ne bayan da ta ziyarci Cibiyar Kula da Cutar Daji (ICCA) da ke Houston a Jihar Tedas ta Amurka a watan Maris din shekarar 2008.
Duk da samun fili da kammala gini da kyaututtuka da dama kamar motoci da suka kai kimanin 100 da Aminiya ta gan su a jibge suna shan rana da ruwa a tsawon shekara takwas, asibitin ya zama kango bayan rasuwar, Shugaba Umaru ’Yar’aduwa. Kuma wasu bayanaii sun ce kayayyakin da aka zuba a asibitin sun yi tsatsa saboda an yi watsi da su.
Lokacin ziyarar Aminiya a asibitin, masu gadi daga kamfanin Habib Security su biyar sun ce ba a ba su damar su bar wani ya shiga asibitin ba, sai dai ta tuntubi Hajiya Turai ’Yar’aduwa in an ba su umarni sai su ba shi damar shiga asibitin.
Wata majiya ta ce akwai zargin barayi sun tsallaka cikin asibitin sun yi awon gaba da wayoyin lantartki da wasu kayayyaki da aka fara sanyawa a asibitin na dimbin kudi.
Hajiya Turai ta fadi a wannan mako cewa, “Abin da ya jawo tsaikon kammalawa da kaddamar da asibitin shi ne rashin cika alkawarin gudunmawar kudi da wadansu suka yi bayan rasuwar mijinta, domin gina asibitin da zai dauki gadaje 200 da dakunan tiyata hudu da sauransu. Baban burina shi ne in ga an kaddamar da asibitin. Bayan kaddamar da gidauniya, mutane sun yi alkawarin ba da gudunmawa, amma da mijina ya rasu, sai suka ki cikawa. Amma mun kammala kashin farko na asibitin domin aiki ne babba. Za mu lalubi wanda ya taba jinyar cutar, domin ya zama shugaban Hukumar Gudanarwar Asibitin saboda zai fi yin himma fiye da wanda bai san cutar ba. Muna da burin fara aiki a asibitin a badi, kuma ba ma son gwamnati ta shigo cikin harkar, domin sarki goma zamani goma, gwamnati na sauyawa, ba mu son dogara da gwamnati. Domin duk wanda yake son cimma burinsa, ya guji dogara da gwamnati.”
Hajiya Turai ta ce, idan asibitin ya fara aiki, zai rage masu zuwa kasashen waje neman magani, kuma talakawa za a yi musu aiki kyauta, sannan masu hali-da-shuni su biya.