✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aguero zai yi bankwana da Manchester City a karshen kaka

Sergio Aguero, dan wasan gaba mafi zira kwallaye a kungiyar Manchester City, zai raba gari da kungiyar a karshen kakar wasanni ta bana bayan karewar…

Sergio Aguero, dan wasan gaba mafi zira kwallaye a kungiyar Manchester City, zai raba gari da kungiyar a karshen kakar wasanni ta bana bayan karewar yarjejeniyarsa.

Cikin wata sanarwar ta kungiyar ta wallafa a shafinta, ta ce Aguero na kasar Argentina mai shekara 32 ba zai sabunta yarjejeniyarsa da ita ba.

A shekarar 2011 Sergio Kun Aguero ya koma Manchester City daga Atletico Madrid wanda ya zira kwallaye 257 a wasanni 384 da ya buga a kungiyar.

Manchester City za ta kafa mutum-mutuminsa a kofar shiga filin wasanta na Etihad a matsayin girmamawa tare da Vincent Company da kuma David Silva saboda bajintar da suka yi mata.

Shugaban Kungiyar, Khaldoon Al Mubarak, ya ce gudunmuwar da Aguero ya bai wa kungiyar ba za ta misaltu ba.

“Duk abin da aka fada a kan gudunmuwar da Aguero ya bayar a City cikin shekaru 10 da ya yi ba a yi karya ba.”

“Gwarzontakar shi za ta kasance abar tunawa a wurin duk wani mai son wannan kungiya ta Manchester City watakila har ma da sauran mutanen da ke kaunar kwallon kafa,” in ji Khaldoon.