Mayakan kungiyar Taliban takwas da soja daya sun mutu bayan ga wasu tara da suka samu raunuka a harin da kungiyar ta kai yankin Darqad na Arewacin Lardin Takhar na kasar Afghanistan.
Kakakin Lardin Takhar, Abdul Khalil Asir ya ce sojojin gwamnatin kasar sun tarwatsa mayakan na Taliban a harin na ranar Asabar, wanda ya bar sojoji biyar da mayakan kungiyar da raunuka.
- Zaben Kano: ’Yan jagaliya sun yi awon gaba da kayan zabe
- Mutane sun tsere yayin da sojoji da Boko Haram ke gwabza fada a Borno
- Abubuwan da ya kamata ku sani game da yakin basasar Najeriya
- Kannywood ta zama kasuwar bukata – Zango
“Mayakan Taliban sun kaddamar da wani babban hari da nufin kwace Hedikwatar yankin Darqad da misalin karfe 01:00 na safiyar yau (Asabar).
“Dakarun gwamnati sun mayar da martani suka tarwatsa maharan da suka cika bujensu da isa bayan an jikkata su,” kamar yadda Abdul ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na Xinhua.
Duk da cewa bai yi cikakken bayanin abin da ya faru ba, wani hafsan soji, Abdul Razeq, ya ce “an kashe mayakan Taliban takwas da soja daya, an kuma jikkkata wasu mutum tara, da suka hada da sojoji biyar, a musayar wutar da aka yi awa biyu ana gwabzawa.”
Mayakan Taliban sun sha yi kokarin neman kwace ikon yankin Darqad ba tare da samun nasara ba a tsawon shekaru.