A ci gaba da wasan kofin nahiyar Afrika da ake yi a kasar Kamaru, Guinea-Bissau za ta fafata da Najeriya.
Sai dai Guinea-Bissau na bukatar doke Najeriya, tare da fatan kasar Masar ta yi rashin nasara a hannun Sudan don samun tikitin zuwa zagaye na gaba.
- Yadda Abacha ya yaudari ’yan Najeriya ya hau mulki —IBB
- Daga Laraba: Hanyoyin Warware Matsalolin Bayan Jefa Kuri’a
Tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta fara gasar AFCON da kafar dama, inda ta fara doke Masar da ci daya mai ban haushi, sannan ta lallasa kasar Sudan da ci 3-1.
Masu sharhi kan harkokin wasanni, musamman gasar kofin Afrika na ganin cewar Najeriya na iya doke Guinea-Bissau duba da yadda suke buga wasa da karsashi.
Tsohon dan Kaftin Super Eagles, Jay-Jay Okocha ya bayyana cewar tawagar ‘yan wasan na iya lashe gasar duba da yadda ta dawo da saka tsoro ga abokan karawarsu.
Shi ma dan wasan gaban Super Eagles, Simon Moses, ya ce ‘yan wasan Super Eagles sun fi murza leda da karkashi karkashin kocin wucin gadi, Augustine Eguavoen.
Guinea-Bissau da Najeriya za su kara da misalin karfe 8 na daren ranar Laraba, a filin wasa na Roumdé Adjia.
Ga jerin tawagar ’yan Najeriya da ke fafata gasar:
Masu Tsaro Raga: Francis Uzoho, John Nobel, Daniel Akpeyi da Maduka Okoye
Masu buga baya: Chidozie Awaziem, Kenneth Omeruo, Leon Balogun; William Ekong; Olaoluwa Aina; Jamilu Collins; Abdullahi Shehu; Zaidu Sanusi da Olisa Ndah.
Masu buga tsakiya: Frank Onyeka; Joseph Ayodele-Aribo, Wilfred Ndidi, Chidera Ejuke, Kelechi Nwakali, Alex Iwobi da Kelechi Iheanacho.
Masu buga gaba: Ahmed Musa, Samuel Chukwueze, Moses Simon, Sadiq Umar da Taiwo Awoniyi.
Ga kuma jerin wadanda ake sa hasashen za su fara yi wa Najeriya wasa:
Uzoho, Aina, Sanusi, Troost-Ekong, Omeruo, Ndidi, Aribo, Onyeka, Chukwueze, Iheanacho da Awoniyi.
Ga jerin tawagar ’yan Guinea-Bissau da ke fafata gasar:
Masu Tsaro Raga: Jonas Mendes, Maurice Gomis, Manuel Mama da Samba Balde.
Masu buga baya: Nanu, Fali Cande, Sori Mane, Leonel Ucha, Simao Junior, Opa Sangatte, Jefferson Encada da Fernandy Mendy.
Masu buga tsakiya: Pele, Bura, Joao Jaquite, Moreto Cassama , Alfa Semedo da Panutche Camara.
Masu buga gaba: Mama Balde, Piqueti, Jorginho, Mauro Rodrigues, Joseph Mendes, Steve Ambri, Frederic Mendy.
’Yan wasan da ake sa hasashen za su fara yi wa Guinea-Bissau wasa:
Mendes, Nanu,Cande, Ucha, Sangatte, Pele, Bura, Semedo, Camara, Balde, Jorginho.