✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2023: Senegal ta lallasa Gambiya 3-0

Senegal da ke kare kambun da ta lashe a 2022 ta fara gasar a bana da kafar dama

Senegal ta lallasa Gambiya da ci 3 da nema a wasan farko na Gasar Nahiyar Afirka na 2023, a rukunin C.

Dan wasan tsakiyar Senegal, Pape Gueye ne ya fara jefa mata kwallo a minti 4 da fara wasa a ragar Gambiya.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci dan wasan gaban Senegal, Lamine Camara ya jefa kwallo biyu a jere; a minti na 52 da 86.

Kafin tafiyar hutun rabin lokaci an bai wa dan wasan tsakiyar Gambiya jan kati.

Korar dan wasan tsakiyar Gambiya ya rage mata karfi, hakan ya sa Senegal ta samu damar kai mata hare-hare da dama.

Sai dai kyaftin din Senegal kuma dan wasan gaban kungiyar Al Nasrr da ke Saudiyya, Sadio Mane bai samu damar zura kwallo a raga ba.

A yanzu dai Senegal ce ke rike da kambun Gasar Nahiyar Afirka, wanda ta lashe a 2022 a bugun fanaretin tsakaninta da Kasar Masar.