✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare barayin janareta 2 a gidan yari a Kano

Alkalin kotun ta dage zaman har zuwa ranar 30 ga watan Janairu, 2024.

Wata Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare wasu mutum biyu a gidan gyaran hali bisa zargin su da satar janareta da kudinsa ya kai Naira 80,000.

Rundunar ’yan sandan jihar, ta gurfanar da wadanda ake zargin mazauna unguwar Dausayi da Warure a Kano, da laifin hada baki da kuma aikata sata.

Tun da farko, mai shigar da kara, Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa wani Sulaiman Magaji ya kai kara ofishin ‘yan sanda da ke Mandawari a ranar 10 ga watan Janairu.

Wada, ya bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun hada baki tare da sace janareta guda daya da kudinsa ya kai Naira 80,000 mallakin wanda ya shigar da karar.

Wadanda ake tuhumar dai sun musanta aikata laifin.

Alkalin kotun, Malam Umar Lawal Abubakar, ya bayar da umarnin ci gaba da tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali na Goron Dutse.

Kazalika, ya dage sauraron karar har zuwa ranar 30 ga watan Janairu, 2024.