✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta yi ajalin mutum 7 ’yan gida daya a Kano

Magidanci da matarsa da kuma ’ya’yansu biyar suka rasu gobarar da ta tashi a sakamakon matsalar wutar lantarki

’Yan gida daya mutum bakwai sun rasu a wata gobara da ta tashi a kusa da Masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara na jihar, Alhaji Saminu Abdullah ne, ya sanar a ranar Litinin cewa wani magidanci da matarsa da kuma ’ya’yansu biyar sun rasu a gobarar.

Abdullahi, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a Kano cewa lamarin da ya faru a daren ranar Lahadi.

“Mun samu kiran gaggawa a ofishin kashe gobara na Dakata daga wani Ibrahim Sani da misalin karfe 12:25 na dare cewa gobara ta tashi a wani gini da ke unguwar Tudun Wada.

“Da samun labarin, muka aike da motar kashe gobara zuwa wurin da misalin karfe 12:30 na dare,” in ji shi.

Ya ce jami’an kwana-kwana sun kwashe mutane bakwai da da gobarar ta rutsa da su, inda suka garzaya da su zuwa asibiti.

“Likita ya tabbatar da mutuwar mutane bakwai sakamakon hayakin da suka shaka,” in ji shi.

Ya kara da cewa bincike ya nuna cewa gobarar ta tashi ne sakamakon wutar lantarki.

Amma ya shawarci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen sarrafa na’urorin lantarki da abubuwan da za su iya kamawa da wuta don guje wa aukuwar gobara.