Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB), Akinwumi Adesina, ya bi sahun masu neman takarar shugaban kasa a zaben 2023 domin maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari.
Rahotanni sun ce wasu kungiyoyin matasa da ’yan Najeriya mazauna kasashen ketare da kungiyoyin mata da manoma da nakasassu da kungiyoyin fararen hula ne suka yi masa karo-karo suka tara Naira miliyan 100 suka saya mishi fom din takara a karkarin jam’iyyar APC.
- Har yanzu ban yanke shawarar fitowa takara ba —Gwamnan CBN
- ’Yan bindiga sun kashe fiye da mutum 50 a Zamfara
Shugaban gamayyar kungiyoyin, Mohammed Saleh, shi ne ya jagoranci kungiyoyin wajen karba wa Adeshina fom kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Shigar Adeshina takarar ya kara yawan masu neman kujerar shugaban kasa jam’iyyar APC a zaben 2023, wadanda yawansu kusa 30.
Adesina, wanda ya kasance Ministan Noma da Raya Karkara a lokacin Gwamnatin PDP da ya kare a 2015, ya ci gaba da kasancewa a kujerarsa ta Shugaban Bankin AfDB, inda Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammad Buhari ta APC ta mara mishi baya.
A baya, wata guguwar badakala ta taso a bankin, inda ake zargin sa da hannu a cuwacuwa, lamarin da ya sa ya koma gefe a ka gudanar da bincike, a yayin da Gwamnatin Buhari ta mara mishi baya ka’in da na’in.
Daga baya kwamitin binciken ya wanke Mista Femi Adesina daga zargin, ya kuma ci gaba da jan ragabar bankin.
Tuni dai salon sayen fom din takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ya ke ci gaba da daukar hankalin mutane, duba da yadda ’yan siyasa daga Aarewa zuwa kudu ke tururuwar sayen fom din takarar da aka sanya kudinsa Naira miliyan 100.