Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya bayyana cewa zai daukaka kara kan hukuncin da Kotun Sauraron Kararrakin Zaben jihar ta yanke na sauke shi daga mukaminsa a wannan Juma’ar.
Aminiya ta ruwaito Kotun sauraron kararrakin zabe a Jihar Osun tana ayyana Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 16 ga watan Yuli.
- Kotu ta soke zaben Adekele a matsayin Gwamnan Osun
- Sau 66 muna dakile yunkurin yi wa taron Majalisar Zartarwa kutse —Pantami
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Olawale Rasheed ya fitar, Adeleke ya sha alwashin kalubalantar hukuncin da ya bayyana a matsayin rashin adalci.
Haka kuma, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Adeleke ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa gaskiya za ta yi halinta a Kotun Daukaka Kara.
Ya ce, “Ina kira ga mutanenmu da su kwantar da hankalinsu.
“Za mu daukaka kara kan hukuncin kuma muna da tabbacin za a yi mana adalci.
“Ina mai tabbatar wa mutanenmu cewa za mu yi duk mai yiwuwa don ci gaba da rike wannan mukami,” in ji Adeleke.