kungiyar ‘Yan Tumatir reshen Jihar Bauchi ta shawarci ‘yan Najeriya da su rika yin addu’o’i ga sabbin shugabannin da aka zaba tunda kan shugaban kasa har zuwa ’yan majalisar dokokin jiha da na tarayya.
Shugaban kungiyar Alhaji Sani Abubakar ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa da ke kasuwar Muda Lawan a ranar Litinin da ta gabata.
Daga nan ya ce za su ci gaba da yin addu’oi musamman ga shugabannin Najeriya domin kowa yasan cewa babbar matsalar da Najeriya ta fuskanta a baya shi ne na rashin shugabanni masu gaskiya da rikon amana.
Daga karshe ya bayyana cewa “kungiyarsa za ta ba da dukkan gudunmawar data kamata ga sabuwar gwamnatin Jihar Bauchi domin ‘yan kasuwa suna da matukar mahimmanci a tsarin zamantakewar al’umma,” inji shi.