✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adawa ba za ta hana mu aiwatar da aikinmu ba —Mai Mala Buni

Shugaban Kwamitin riko na jam’iyyar APC kuma Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ce bukatar ya ajiye shugabanci da wasu ke yi, ba za…

Shugaban Kwamitin riko na jam’iyyar APC kuma Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ce bukatar ya ajiye shugabanci da wasu ke yi, ba za ta dau hankalinsa ba daga aiwatar da aikin da a ka bai wa kwamitinsa na sasantawa da kuma sake dawo da wadanda su ka fusata suka bar jam’iyyar.

Shugaban na APC ya yi bayanin ne a ranar Litinin a Birnin Abuja, a lokacin da ya ke karbar wani dan siyasa daga jihar Adamawa Alhaji Abdurrahman Buba Kwaccham da ya sauya sheka zuwa APC daga jamiyyarsa ta SDP a kwanakin baya.

Ya ce aikin da kwamitin ya aiwatar tun lokacin da ya karbi shugabanci a bayyana ya ke, kuma gamsuwa da hakan ne  ya sa Kwamitin koli na jam’iyyar wato NEC, ya basu wani sabon aiki na gudanar da zaben sabbin shugabannin jam’iyyar daga matakin jiha zuwa na tarayya.

Mai Mala Buni ya ce shi da Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello da kuma na Osun Cif Gboyega Oyetola, da Majalisar Koli ta jam’iyar ta dora wa nauyin kuma za su gudanar da aikinsu cikin adalci.

Ya kuma bayyana farin ciki a kan shigowar Buba Kwaccham cikin jam’iyar, inda ya bayyana hakan a matsayin babban kamu ga jam’iyyar.

A jawabin da ya yi, Abdurrahman Buba Kwaccham wanda ya ce ya shiga jam’iyyar ne kan bukatar wasu jagorori daga jiharsa ta Adamawa tare da amfani da hakan wajen kai ayyukan ci gaba a yankin, ya kuma yaba da salon siyasa irin na Gwamna Mai Mala, kan sasanci da kuma rungumar kowa.