✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adamawa: Sanarwar ‘nasarar Binani’ daidai ne —Kwamishinan Zabe

A wasikarsa ga Shugaban ’Yan Sandan Najeriya da ke nemansa, Hudu ya ce ya sanar da sakamakon zaben ne saboda dalilan tsaro

Kwamishinan zaben Jihar Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa Ari, ya bayyana cewa sanarwar da ya yi cewa Sanata Aisha Binani ce ta yi nasara a zaben da aka karasa ranar 15 ga wata bai saba doka ba.

A wasikarsa ga Shugaban ’Yan Sandan Najeriya da ke nemansa, Hudu, wanda lauya ne ya ce ya sanar da sakamakon rumfuana 69 da aka karasa zaben ne saboda dalilan tsaro.

Sanarwarsa cewa Binani ta jam’iyyar APC ta doke Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP ya tayar da kura, har Hukumar Zabe na Kasa (INEC) ta dakatar da tattara sakamkon zaben, ta dakatar ta shi tare da neman  ya bayyana a hedikwatarta da ke Abuja. Daga baya ta bukaci shugaban ’yan sanda ya binciki Hudu.

Amma a wasikarsa ga shugaban ’yan sandan, Hudu ya bayyana cewa, abin da ya yi bai saba doka ba, saboda ya yi ne domin  kauce wa barazanar da ke tattare da jinkirin sanar da sakamakon.

A cewarsa, sakamakon da jami’an tattara sakamkon zaben rumfuna 69 da aka yi karashen zaben sun sha bambanta da wanda aka sanya a shafin sakamakon zaben INEC na IReV, don haka ya ki sanya hannu a kai.

A wasikar, wadda ya tura wa shugaban INEC, da hukumar tsaro ta DSS kwafi, kwamishinan zaben da aka dakatar ya bayyana ce barazanar da ya fuskanta sun hada da barazanar wasu ’yan takara na tayar da rikici da kuma yadda ’yan sanda daga gidan gwamnatin jihar suka yi wa gidansa kawanya.

Bugu da kari, akwai yunkurin maye gurbinsa da Sakataren Gudanarwan INEC na jihar da kuma shirin wasu kwamishinoi na nadan ‘jami’an tattara sakamakon zabe ba bisa ka’ida ba’.

Ya bayyana cewa, “Wadannan ne suka sa na ta tttara sakamakon rumfunan zaben sannan na sanar da cewa ’yar takarar APC ce ta yi nasara saboda ita ce ta samu kuri’u mafi rinjaye.

“Da ma can ina da alkaluman kuri’un kowanne daga cikin manyan ’yan takarar biyu suka samu shi a karashen zaben, kamar yadda yake rubutce a takardar sakamakon zabe da halastattun turawan zabe tare da ni, a matsayina na Kwamishinan Zabe kuma Babban Mai Tattara Sakamakon Zabe na Jihar Adamawa.

“Kafin nan, na samu bayanan sirri cewa a cikin daren 15 ga wata wasu kwamishinonin zabe na kasa guda biyu sun je gidan gwamnati da ke Yola inda suka tattauna da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.”

A cewar Barista Hudu, sanarwar da ya yi ke da wuya, wasu magoya bayan PDP suka kai wa kwamishinonin zaben da baturen zaben hari, saboda sun kasa yin abin da gamnan ya nema.

Ya kara da cewa, “Ana zargin muanen da aka yi wa duka a wani bidiyo, “su ne suka so murde abin da mutaen Adamawa suka zaba a karashen zaben da aka yi.”