Samun adalci daga wurin Allah ba daga namu ayyuka ba, shi ne kadai irin adalcin da zai gamsar da Ubangiji Allah, wannan ita ce shirin Allah tun daga farko: “Shi wanda ba ya son kowane zunubi ba, ya maishe shi zama zunubi saboda mu; domin mu zama adalcin Allah a cikinsa.”(2 Korinthiyawa 5:21). Ashe akwai wuri daya kawai da za mu iya samun wannan adalcin; wato bin Yesu Kiristi kawai. Sai mu lura fa, ba dukkan wanda yana zuwa sujada shi ne Kirista ba, amma sai wanda yana aikata nufin Allah bisa ga maganarsa: “Ba dukkan mai ce mini Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga cikin mulkin sama ba; sai wanda ke aika nufin Ubana wanda ke cikin sama.”(Matta: 5: 21). Mutane da yawa sukan nuna wa sauran jama’a kamar su masu tsoron Allah ne, amma gaskiyar ita ce, masu mugunta ne, babu tsoron Allah a cikin zuciyarsu ko na kwabo. Irin wadannan mutane ba za su iya yin gaskiya ba domin cike suke da yaudara.
Yayin da nauyin shugabanci ya rataya bisa wadanda ke rike da mukamai daban-daban, sauran mutane da ke karkashinsu, su ma suna da nauyin da ya rataya a kansu. Abin da in Allah Ya yarda za mu tattauna a kai yanzu.
Mene ne Ubangiji Allah Yake so mu talakawa mu yi domin mu samu shugabanni nagari? Abu mai sauki ga mutum ya ga kuskuren wadansu, musamman ma na wadanda suke kan mukamai daban-daban; yawancin lokaci, talakawa sukan zargi shugabanni, su kuma dora musu laifi. Kowane shugaba yana sane da wannan; duk lokacin da abu ya lalace abu mai sauki ne a dora musu laifin! Abu daya da yawancin lokaci akan manta shi ne, mene ne ya kamata mu yi domin mu samu shugabanni nagari, masu tsoron Allah da za su yi abin da yake daidai domin gina kasa? Maganar Allah na koya cewa: “A farkon farawa dai ina umarni a yi bidebide da addu’o’i da roke-roke da godiya, saboda dukkan mutane, domin sarakuna da dukkan wadanda ke cikin matsayin manya; domin mu yi ranmu mai natsuwa da hankali kwance cikin dukkan ibada da kintsa fuska. Wannan mai kyau ne, abin karba kuwa ga Allah Mai cetonmu; Shi wanda Yake nufin dukkan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.”(1Timo: 2 : 1 – 5).
Abu muhimmi na farko da ya kamata kowane mutum ya yi wa shugabanni, shi ne addu’a; idan har muna so shugabannin su yi abin kirki, dole sai mun mika su ga Allah a koyaushe domin su iya cin nasara game da jarabawar da suke fuskanta yau da kullum. Kada mu dora musu laifi haka kawai, wani lokacin ba da son su ba ne, abin ya fi karfinsu ne. Misali idan ’yan siyasa suka taru wuri daya, kowa da nasa ra’ayin, ba lallai ne su yi abin da kake so ba, a karshe abin da yawancin mutanen da ke wurin suka zartar, shi za a yi, koda ba shi ya dace ba. Babu yadda za a samu al’umma mai albarka, mai jin tsoron Allah ba tare da yin addu’a ba. Na lura sau da dama; mutane sai guna-guni suka iya duk lokacin da suka ga abu ba ya tafiya daidai yadda ya kamata. Guna-guni ba ya taba kawo canji ko kadan a ko ina, surutu ne kawai marar amfani, Allah Shi kadai ke iya kawo mana taimako, kuma Yana shirye domin Ya ji addu’o’inmu.
Me ya sa mutane da yawa ba su ga dalilin komawa ga Allah cikin yin addu’a da kuka domin wannan kasar ba? Abu daya ne kawai shi ne rashin kula. Mutane sai guna-guni suka iya, shi ke nan, babu wani abin da suke yi kuma. Abu na biyu shi ne, mutane da yawa ba su ma gane irin hadarin da muke ciki a wannan kasar ba har yanzu. Idanunsu a rufe suke, bari mu ga wani abu kadan daga cikin Littafi Mai tsarki da zai nuna mana irin yanayin da muke ciki a kasarmu: “Maganar Ubangiji ta zo gare ni kuma cewa, dan mutum, ka ce mata ke kasa ce da ba a tsarkake ba, ba a yi miki ruwan sama ba a ranar fushi. Akwai makidar annabawanta a cikinta kamar zaki mai ruri yana yayyage naman ganima: sun cinye rayukan mutane; sun kwace kayan ajiya da na tamani; sun yawaita gwauraye a ciki.
Priests nata sun bata shari’a, sun tozartar da abin da ke mai tsarki gare ni; ba su bambamta tsakanin mai tsarki da mara tsarki; ba su kuwa sa mutane su bambanta mara tsabta da mai tsabta ba; sun rufe idanunsu, da ba za su lura da sabbataina ba, ni ma na tozartar da ni a cikinsu. Hakimanta a cikinta kamar kerketai ne masu yayyage naman ganima, suna zub da jini, suna halaka rayukan mutane, domin su ci kura da zamba. Annabawanta kuma sun yi musu shafi da farin kitse, suna yi musu ru’uyar wofi, da dukkan karya suna cewa, inji Ubangiji Yahweh; Ubangiji kuwa bai fadi ba. Mutanen kasa sun yi aikin zalama, sun yi kwace; Eh, sun wahalar da talakawa da masu mayata, sun yi wa bako zalama ba kan shari’a ba. Na kuwa nemi mutum daya daga cikinsu, wanda za ya gyara ganuwa, ya tsaya a wurin tsaguwa a gabana domin ceton kasa, kada in halaka ta: amma ban samu ba”. (Ezekiel 22: 23 – 30).www
Adalci: Tushen gina al’umma mai albarka II
Samun adalci daga wurin Allah ba daga namu ayyuka ba, shi ne kadai irin adalcin da zai gamsar da Ubangiji Allah, wannan ita ce shirin…