Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da karin rasuwar wasu mata uku da suka samu rauni a wajen turmutsitsin rabon Zakka a Jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa akalla mutum 10 ne suka rasu a wajen rabon zakkar a ranar Lahadi a ofishin AYM Shafa.
- Jami’in Binance ya tsere daga hannun mahukuntan Nijeriya
- Harkar Noma Ce Kaɗai Za Ta Samar Da Zaman Lafiya A Najeriya — Peter Obi
Amma tun da fari rundunar ’yan sandan jihar ta ce mutum hudu ne kawai suka rasu a wajen turmutsitsin a ranar Lahadi.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Ahmed Wakili, ya tabbatar da wannan ci gaban a ranar Litinin.
Ya ce, “Likitoci a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), sun tabbatar da mutuwar karin mata uku.”
Wakil, ya bayyana sunayen wadanda suka rasu, Aisha Usman, mai shekara 13, Sahura Abubakar, mai shekara 55, Aisha Ibrahim Abubakar, mai shekara 43 da kuma Khadija Isah ’yar shekara takwas.
Sauran wadanda suka rasu, su ne Maryam Suleiman, mai shekara 20, Maryam Shuaibu, mai shekara 16, da kuma Hassana Saidu mai shekara 53.
Wakil ya kara da cewa, “Wadannan su ne adadin wadanda abin ya shafa kuma likitoci sun tabbatar da rasuwarsh. Za mu yi wa jama’a karin bayani daga baya.”