✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Adadin mutanen da suka mutu a harin Masallacin Pakistan ya kai 61

Kawo yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.

Adadin mutanen da suka mutu a kazamin harin da aka kaddamar kan Masallaci a Pakistan ya kai 61 kamar yadda mahukunta suka tabbatar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ya hada da jami’an ’yan sanda, yayin da kimanin 150 suka jikkata.

An kai harin ne a lokacin da jama’a suka hallara domin gudanar da Sallar Azahar a Masallacin da ke shalkwatar Jami’an ‘yan sandan Pakistan a birnin Peshawar da ke kusa da kan iyakar Afghanistan mai fama da ayyukan ta’addanci.

Yanzu haka ana ci gaba da aikin agaji a Masallacin wanda daukacin garunsa da rufinsa suka tarwatse a dalilin karfin fashewar da ta auku a yayin farmakin.

Shugaban Rundunar ’Yan sandan Peshawar, Mohammed Ijaz Khan ya ce, kimanin jami’an ‘yan sanda 300 zuwa 400 ke yawan halartar Masallanci a kullum, kuma buraguzai sun danne da dama daga cikinsu a sanadiyar harin na yau.

Motocin Asibiti sun yi kwasar gawarwakin mutanen da suka rasu, sannan an ga yadda wadanda suka tsira da rayukansu ke ta dingisawa bayan sun yi jina-jina sakamakon buraguzan da suka fado musu.

Tuni dai hukumomi suka sanya kasar cikin gagarumin shirin-ko-ta-kwana bayan wannan harin na bam, inda aka zafafa bincike a shingayen ababen hawa tare da jibge karin jami’an tsaro a wasu wurare.

Kazalika an girke jami’an tsaro na musamman da suka kware wajen harbi da bindiga a babban birnin Islamabad.

Firaministan kasar, Shehbaz Sharif ya ce “’yan ta’adda na son sanya tsoro da fargaba a zukatan al’umma ta hanyar kai hari kan jami’an da ke kare kasar Pakisatan.”

Kawo yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, to sai dai ana alakanta shi da ’yan kungiyar Taliban ta Pakistan.

A watan Nuwamba ne dai kungiyar ta kawo karshen tsagaita bude wuta, daga nan ne kuma aka fara samun hare-hare a kasar.

Ko a watan Disamban bara ma ta kai hari kan wani ofishin ’yan sanda a Arewa maso Yammacin kasar lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan bindiga 33.