Ofishin Kiyaye Hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya (OHCHR) ya ce akalla yawan fararen hular da aka kashe tun da aka fara rikici tsakanin kasashen Rasha da Ukraine ya haura 5,000.
Kwamishiniyar hukumar, Michelle Bachelet Jeria, wacce ta bayyana alkaluman ranar Talata ta kuma ce akwai harsashen yiwuwar karuwar adadin a nan gaba.
- Akwai ’yan Boko Haram 61,000 tsare a gidajen yarin Arewa maso Gabas – Aregbesola
- ‘Ko sisi ba a biya ba don sako fasinjojin jirgin kasan Kaduna su 7’
Ofishin dai wanda ke da gwamman masu sa ido da tattara alkaluma a kasar ya bayyana a cikin rahotonsa na mako-mako cewa ya zuwa yanzu, mutanen da aka kashe sun kai 5,024, yayin da wadanda aka jikkata suka kai 6,520.
A wani labarin kuma, kasar Amurka ta ce za ta aike wa Ukraine karin kudaden tallafi da yawansu ya kai Dalar Amurka biliyan daya da miliyan 700.
Ana sa ran Ukraine ta yi amfani da tallafin wajen tayar da komadar tattali arzikinta wanda rikicin ya daidaita.
Sakatariyar baitil-malin Amurka, Janet Yellen ta fada a cikin wata sanarwa cewa, “Wannan tallafin zai taimaka wa gwamnatin Ukraine ta samar da abubuwan more rayuwa ga mutanen kasarta.”
Kudaden dai na cikin kason Dala biliyan bakwai da miliyan 700 din da Shugaban Amurka, Joe Biden, ya rattaba wa hannu a watan Mayun da ya gabata.
Tun a ranar 24 ga watan Fabrairun da ya gabata ce dai Rasha ta kaddamar da kai hare-hare a kan Ukraine, lamarin da ya kai ga jikkata dakaru da fararen hula da dama, yayin da wasu miliyoyi suka rasa muhallansu.