Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin Naira tiriliyan 13.08 na shekarar 2021 a gaban Majalisar Tarayya.
A jawaninsa yayin mika daftarin kasafin, shugaban kasar ya ce an yi kasafin ne a kan farashin gangar danyen mai Dala 40 da kuma hasashen hako gangar mai miliyan 1.86 a kullum.
- Buhari ya mika wa Majalisa kasafin 2021
- Zan yi mulki tare da kowane bangere —Sarkin Zazzau
- ‘Ina da kwarin gwiwa a kan sabon sarkin Zazzau’
Kasafin da aka yi a kan canjin Dala N379 na hasashen samun karuwar kayan da ake samarwa a cikin gida da kashi uku, sai hauhawar farashi da kasha 11.
Jimillar kasafin na Naira tiriliyan 13.08 ya haura na 2020 da aka yi wa gyaran fuska zuwa tirilyan 10.805 da Naira tiriliyan 2.28.
Ya yi hasashen samun kudaden shiga na Naira tiriliyan 7.89 da gibin Naira tiriliyan 4.4.
Kashi 29 dinsa (tiriliyan 3.58) an ware ne domin manyan ayyuka sabanin kashi 24 da aka ware a 2020.