Karar wani abun fashewa da ya yi bindiga ya girgiza Riyadh, Babban Birnin Kasar Saudiyya.
An ji abun fashewan ya yi bindiga ne a ranar Talata sai dai babu bayani game abin da hakikanin abin da ya faru, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ba da rahoto.
Gidan Talabijin na Al Arabiya TV na kasar Saudiyya ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na sa da zumunta da ke nuna rokoki da aka harbo a sararin samaniyan birnin Riyadh.
A ranar Asabar, rundunar hadin gwiwar kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta domin yakar ‘yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun harbo rokokin da aka harba zuwa Riyadh.
Sanarwar da rundunar ta fitar ce ce rundunar ta harbo wasu rokoki da “makiya” da suka nufi Riyadh.