✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shin kun san abin da ya kawo tsadar kayan abinci?

Majalisar Samar da Abinci ta Kasa ta alakanta tsadar kayan abincin da ake fama da ita da yawan kayan amfanin gonar da aka saya don…

Majalisar Samar da Abinci ta Kasa ta alakanta tsadar kayan abincin da ake fama da ita da yawan kayan amfanin gonar da aka saya don raba wa jama’a a matsayin tallafin COVID-19.

Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar wanda ke wakiltar Arewa maso Yamma a majalisar ne ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyin ‘yan jarida a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Ya ce yawan kayan abincin da gwamayyar kungiyoyin yaki da cutar (CACOVID), Gwamnatin Tarayya da na jihohi suka saya domin raba wa mabukata ya taimaka wajen kawo tsadar abincin.

Sai dai kuma ya bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba farashin kayan zai sauka saboda kaka na dada matsowa.

“Bari na yi muku karin bayani kan makasudin tashin gwauron zabin kayan abinci.

“Ba za ka ga farashin ya sauka ba musamman ga wadanda suke zaune a birane irinsu Abuja ba, dole sai a hankali.

“Amma a kasuwannin kauyuka yanzu haka kayan na kara sauki amma dole sai an saya an kuma yi jigilarsu.

“Idan kuma dan kasuwa na da ajiyayyun kaya, ba zai yiwu ya yi asara ya karyar da farashinsu ba, dole sai ya jira sun kare tukuna.

“Idan ya kasance an samu wadatar kayan a kasuwa kuma to dole farashin nasu zai sauka”, inji Badaru.

To sai dai Mataimakin Shugaban Majalisar kuma Jwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya ce farashin kayan yanzu haka na sauka kamar yadda alkaluma suke nunawa.

Ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin rage farashin buhun takin zamani daga N5,500 zuwa N5,000.

%d bloggers like this: