Ga bayanin abubuwan da za ku so sani game da ’ya’yan Manzon Allah (SAW), matansa da kuma iyalan gidansa (Ahlul baiti) a takaice.
Matan Manzon Allah su ne kamar haka:
1. Saudatu bint Zam’ah (RA):
Annabi (SAW) ya aure ta a watan Shawwal bayan shekara 10 da aiko shi da manzanci.
Mijinta ya rasu a Habasha kuma kulawa da rayuwarta ya koma hannun gyatumarta wadda a lokacin ta tsufa.
Tana daga cikin wadanda
suka musulunta suna manya. Ita Manzon Allah (SAW) ya fara aure bayan rasuwar Khadijah.
Ta zauna da Manzon Allah (SAW) tsawon shekara 13, kuma ta rasu shekara 54 Bayan Hijira.
2. A’ishatu (RA):
A’ishatu (RA) ’yar Abubakar Siddik (RA), babban abokin Manzon Allah
(SAW) kuma Khalifansa na farko.
Annabi (SAW) ya aure, gab da zai yi hijira, tana da shekara 6 ko 7, ya kuma tare da ita tana da shekara 9.
Ita kadai ce Manzon Allah (SAW) ya aura tana budurwa.
Ta taka rawa a fagen ilimi kuma Annabi (SAW) ya nemi izinin matansa don ya yi jinyar ajali a dakinta.
Don haka a dakinta ya yi jinya, a dakinta ya rasu kuma a dakinta aka binne shi.
Ta zauna tare da Manzon Allah (SAW) tsawon shekara 13, kuma
ta rasu ne a cikin watan Ramadan shekara ta 58 Bayan Hijira.
3. Hafsat bint Umar Al-Khattab
(RA):
Annabi (SAW) ya aure ta a watan Sha’aban shekara ta 3 Bayan Hijira kuma ta rasu a watan Sha’aban shekara ta 45 Bayan Hijira.
Ta zauna tare da Manzon Allah (SAW) tsawon kimanin shekara takwas.
4. Zainab bint Khuzaimah (RA:
Ita ake kira ‘Ummul Masakin’ saboda yawan alherinta da ciyar da
miskinai.
Annabi (SAW) ya aure ta a shekara ta 5 Bayan Hijira.
Ta rasu Annabi (SAW) yana raye, ta yi wata takwas ne kawai da Annabi
(SAW) sai Allah Ya yi mata rasuwa.
5. Ummu Salamah Hindu bint Abu Umayyah (RA):
Tana daga cikin wadanda suka yi hijira sau biyu (ta yi hijira zuwa Habasha) tare da mijinta.
Mijinta ya rasu a Yakin Uhud, kuma Annabi (SAW) ya aure ta a watan Shawwal shekara ta 4 Bayan Hijira.
Ta rasu a shekara ta 59 Bayan Hijira.
6. Zainab bint Jahshin (RA):
Annabi (SAW) ya aure ta a watan Zil-Kida shekara ta 5 Bayan Hijira, lokacin tana da shekara 35; Ta rasu a shekara ta 20 Bayan Hijira.
Ita ce ayoyin Alkur’ani suka sauka game da aurenta: “Kuma a lokacin da kake cewa ga wanda Allah Ya yi ni’ima a gare shi, kuma kai ma ka yi ni’ima a gare shi, ka riki matarka, kuma ka bi Allah da takawa. Kuma kana boyewa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana, kana tsoron mutane, alhali kuma Allah ne Mafi cancantar ka ji tsoron Sa. To a lokacin da Zaidu ya kare bukatarsa daga gare ta, Mun aurar maka da ita…” (Ahzab:37).
7. Juwairiyyah bint Haris (RA):
Tana daga cikin ribatattun yaki da Manzon Allah (SAW) ya sa aka saki, kuma ta fito ne daga gidan daya daga cikin jagororin kabilarsu.
Annabi (SAW) ya aure ta a watan Sha’aban a shekara ta 6 Bayan Hijira, bayan an ’yanta ta.
Ta rasu a shekara ta 50 Bayan Hijira.
8. Ummu Habibah Ramlatu bint Abu Safyan (RA):
Mijinta na farko ya rasu a Habasha, ita ce wadda Sarki Najjashi ya aiko sadakinta ga Annabi (SAW).
Ya aure ta a shekara ta 7 Bayan Hijira, kuma ta rasu a shekara 44 Bayan
Hijira.
9. Safiyyah bint Huyyayi (RA):
Babanta shi ne Shugaban Yahudawan Banu Nazir.
Annabi (SAW) ya aure ta a shekara ta 7 Bayan Hijira; Ta rasu a shekara ta 50 Bayan Hijira.
10. Maimunatu bint Haris (RA):
Annabi (SAW) ya aure ta a watan Zul-Kida a shekara ta 7 Bayan Hijira, kuma ta rasu a shekara ta 61 Bayan Hijira.
Wadansu malaman tarihi sun kara da cewa Annabi (SAW) ya auri Ummu Shuraik Al-Ansariyya, amma bai tare da ita ba.
Kuma ya auri Aliya bint Zabyan amma ya sake ta sannan akwai wadanda ya yi sadaka da su a matsayin bayinsa.
Waxannan kuma su ne Mariyatul Kibxiyyah da Raihanatu bint
Sham’un.
Amma dukkan wadannan da suka karu a kan 11 na farko, malaman tarihi sun yi sabani a kansu. Wallahu a’alam.
’Ya’yan Manzon Allah (SAW)
Dangane kuma da ’ya’yan Ma’aiki (SAW), magana mafi shahara ita ce Manzon Allah (SAW) ya haifi ’ya’ya bakwai ne a duniya, haka Almakdisiy ya ce a cikin kaulinsa.
Wadannan ’ya’ya kuwa sun kunshi maza uku da mata hudu, kamar haka:
1. Al-Qasim:
An haife shi shekara biyu kafin a aiko Manzon Allah (SAW) da manzanci.
Da shi Al-Qasim ake yi wa Manzon Allah (SAW) alkunya, wato ake kiransa da Abul-Qasim, kuma Allah Ya yi masa rasuwa bayan ’yan kwanaki a duniya.
2. Abdullahi:
Ana kiran sa Attayyib ko kuma Attahir.
An haife shi a cikin Musulunci, kuma shi ma ya bar duniya bai yi shekaru da yawa ba.
3. Ibrahim:
An haifi Ibrahimul Mu’azzam a garin Madina, kuma shi kadai ne ba dan Khadijah (RA) ba a cikin ’ya’yan Manzon Allah (SAW).
Mahaifiyarsa ita ce kuyangar Annabi (SAW) mai suna Mariyatul-Kibxiyya.
Ya rasu yana da wata takwas a duniya.
4. Zainab:
Ita ce babbarsu, kuma ta auri Abdul Ass bn Arrabi’a bn Abdul Uzza.
5. Ruqayyah:
Ta auri sahabi kuma Khalifan Manzon Allah (SAW) Usman bin Affan (RA).
6. Fadimatu:
Ta auri Aliyu bin Abu Dalib, kuma ’ya’yanta biyu wato Al-Hassan da Al-Hussain su ne shugabannin samarin gidan Aljanna.
7. Ummu Khulsum:
Bayan rasuwar Rukayyah ita aka aurar wa Usman bin Affan (RA), sannan ya sa ake kiransa Zun-Nuraini, wato ma’abocin haske biyu.
Matsayin Iyalan Gidan Manzon Allah (SAW)
Babu shakka matsayin Manzon Allah (SAW) a cikin al’ummarsa
matsayi ne mai girma.
Mun riga mun ji irin daraja da daukakar da Allah (SAW) Ya yi wa Manzon
Allah (SAW).
Baya ga Manzon Allah (SAW), har ila yau Allah Ya daukaka darajar wadanda suke kewaye da shi.
Mun ji matsayin sahabban Manzon Allah (SAW) da fiffikonsu bisa sauran Musulmi.
Kamar yadda sahabban Manzon Allah (SAW) suka samu shaidar fiffikon daraja a tsakanin al’ummar Manzon Allah (SAW), haka ma Allah Ya daukaka darajar Mutanen Gidan Annabi (SAW),
Mutanen Gidan Manzon
Allah (SAW) su ne iyalan gidansa ko ‘ahlul-bait’ kamar yadda yake a wajen ambato.
Wannan kuma sun hasa da matansa da ’ya’yansa da danginsa na jini da suka hada da iyalan Aliyu da iyalan Akilu da iyalan Ja’afar da kuma yalan
Abbas (RA).
Alkur’ani Mai girma ya ambaci iyalan Manzon Allah (SAW) kai-tsaye a lokacin da ake magana game da matan Annabi (SAW).
Allah (SWT) Ya ce: “Kuma ku tabbata a cikin gidajenku kada ku yi fita irin fita ta Jahiliyyar Farko. Kuma ku tsai da Sallah, ku bayar da zakka, ku yi da’a ga Allah da Manzon Allah. Allah Yana nufin ya tafiyar da kazanta daga gare ku, Ya Mutanen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku tsarkakewa.” (Ahzab: 33).
A karkashin bayanin wannan aya mai girma, sahabban Manzon Allah (SAW) da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa suka tafi kan cewa lallai matan Manzon Allah (SAW) suna daga cikin Ahlul-baitinsa.
Domin kalmar ahlul baiti da ke cikin ayar tana magana ne kai-tsaye da matan Manzon Allah (SAW), iyayen muminai.
Bayan matan Manzon Allah (SAW), hadisai masu inganci sun shigar da wadansu rukuni na mutanen gidan Manzon Allah (SAW) cikin mutanen Babban Gida.
Mun tsakuro wannan rubutu ne daga littafin Farin Jakada na Malam Aliyu Gamawa, (+2348023893141).
email: aliyugamawa@gmail. com