Amfani da jiragen ruwa ta haramtacciyar hanya da tafiyar dare da rashin amfani da rigar kariya a kan ruwa da sauransu, su ne sabubban yawaitar nitsewar jiragen ruwa Neriya.
Manajan Daraktan Hukumar Hanyoyin Ruwa Na Cikin Kasa (NIWA), George Moghalu, ya ce kashi 80 cikin 100 na hatsarin jiragen ruwa a Najeriya na faruwa ne da dare ko da safe, lokacin da yanayi ba shi da kyawu.
Jami’in ya ce, “Hadarin jiragen ruwa abin takaici da kunya ne kuma abin tsoro ne jin labarin yawan hadarin jiragen ruwan da kan rutsa da ’yan Najeriya.”
Ya ce duk da kokarin hukumar na gargadi kan tafiya a kananan jiragen ruwa da dare, bai hana wasu ’yan kasar, musamman ’yan kasuwa da ke kara jefa rayuwarsu cikin hadari.
Moghalu ya kara da cewa, sakaci da daukar mutane da kaya fiye da kima da gudun wuce misali da rashin kyawun yanayi da sauransu, na daga cikin dalilan da kan haifar da hadarin jirgin ruwa Najeriya.
Ya bayyana wa wani taron manema labarai a Abuja cewa domin takaita aukuwar hadarin jirgin ruwa a Nejeriya, NIWA ta bada himma wajen samar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen cim ma haka.
Tsare-tsaren sun sun hada da horar da matuka jirgin ruwa da tabbatar da bin doka da oda da wayar da kan ’yan kasa da sauransu.