A ranar Asabar da ta gabata ne Cibiyar Ufuk Dialogue Foundation mai hedikwata a Turkiyya da kuma Ma’aikatar Al’adu da Yawon Bude Idanu da kuma Wayar da kan Jama’a ta Tarayya suka shirya bikin hadin gwiwa na al’adar kasar Turkiyya da kuma Najeriya a Abuja.
Wannan shi ne karo na hudu da aka shirya bikin, wanda kuma ya kayatar da jama’a.
Bikin wanda ya kunshi raye-raye da kade-kade da wake-wake ya samu halartar jama’a daga Najeriya da Turkiyya da kuma sauran kasashen duniya.
A yayin bikin an nuna irin tufafin kasar Turkiyya da Najeriya. Daga Najeriya an nuna al’adar manyan yarukan uku da suka hada da Hausa da Ibo da kuma Yarabanci.
An kuma nuna abincin kasar Turkiyya da suka hada da Acıbadem da Aşure da Ayba tatlısı da Badem ezmesi (Marzipan) da Baklaba da Bülbül Yubas da Menemen da sauransu.
Dangane da tufafin kasar Turkiyya kuma akwai na mata da suka hada da Goddiba da Ceme da bero Moda; na maza kuma akwai huluna da sauran riguna da wanduna.
A cikin kayayyakin da kabilar Ibo ta kawo akwai Akwu da Turmi da Ede da Achi da Okobo da sauransu.
Kayayyakin da Hausawa suka nuna sun hada da Babbar riga aska tara da murjani da jakankuna fata da ragaya da zobba da shimfidun gidan sarauta da sauransu.
Wani abu da ya burge jama’a shi ne, yadda wata dalibai ‘yar shekarar 12 mai suna Nanzi Haruna daga Kwalajen Turkiyya da Najeriya da ke Kaduna ta rera wakar Turkiyya. Jama’a suka rika ihu da sowa, sannan aka gayyato wadansu yara ’yan Turkiyya suka rera waka da yaren Ibo.
Bayan nan sai aka gayyato mawakan Caucasian daga kasar Turkiyya, inda suka nishadantar da taron
An gudanar da gasar rawa da waka inda masu rawa daga kabilar Hausawa suka lashe gasar, sai Yarabawa da kuma Ibo .
Darakta a Ma’aikatar Al’adu da yawon bude idanu ta Tarayya George Efuk ne ya wakilci Ministan Ma’aikatar Edem Duke, inda ya ce wannan bikin na kara yaukaka zumunci da kuma kara dankon dangantaka tsakanin kasar Turkiyya da kuma Najeriya.
“Abin a yaba wa wadanda suka shirya wannan bikin ne, domin yana kara dankon dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da kuma Najeriya. Dole na yaba wa Fethullah Gelen da ya kafa makaratu, ya gina asibitoci da kuma masana’antu a kasar nan, wadanda suka bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu.” Inji Efuk.
Ya ce, ya samu damar ziyartar Turkiyya a wani lokaci, ya ga abubuwan mamaki da daukar hankali da kuma kayartarwa a kasar. Mutanen kasar na son zama lafiya, suna da hakuri da juriya da al’adu masu yawa da kuma kimiyya da fasaha. “Muna yaba muku yadda jama’arku da ke nan suka taimaka wajen bunkasa kasar nan ta bangarori da suka hada ilimi da lafiya da kuma muhalli.”
Hajiya Saudatu mai ba mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo shawara a Majalisar Tarayya ce ta wakilci matar mataimakin shugaba kasa Amina Namadi Sambo a wajen taron, inda ta ce an shirya taron ne don a gina gadar za ta kara hada kan kasashen biyu.
“Muna da labarin Nasriddin Hoja dan kasar Turkiyya wanda a Arewacin Najeriya ake kiransa da Shehu Jaha. An karu da fasaha da fikira da wayonsa a arewacin kasar sakamakon labaransa. Don haka wannan ba taron shan shayi ba ne sai don a samar da gadar da za ta kara hada kan kasashen.
Jama’ar da suka halarci bikin sun ce sun ga abubuwan da suka burge su, sun nishadantu, sun kuma fa’idantu.
Abubuwan burgewa a bikin al’adun Turkiyya da Najeriya
A ranar Asabar da ta gabata ne Cibiyar Ufuk Dialogue Foundation mai hedikwata a Turkiyya da kuma Ma’aikatar Al’adu da Yawon Bude Idanu da kuma…