Shiga harka noma ka’in da nau’in ta fuskar kasuwanci na bukatar la’akari da wasu muhimman abubuwa domin samun nasara, ba wai yawan jari na kudi ba.
Tsayawa tsam tare da yin nazarin hali da kuma yanayin da kake ciki kafin ka tsunduma kasuwanci, shi ne mataki na farko.
- An jibge jami’an tsaro 40,000 albarkacin zaben gwamna a Kogi
- Kimiyya ce ginshikin ci gaban duniya – UNESCO
Hakuri da juriya da mai da hankali da aiki tukuru da kuma tafiya da fasahar zamani sinadarai na samun nasara muddin aka kiyaye su kamar haka:
Hakuri
“Mai haƙuri shi ke dafa dutse ya sha romonsa” inji masu iya magana, kuma haka yake ko a harkar noma don riba haka batun yake, musamman a zamanance a kuma kamfanance.
Kasancer komai yana da tsari da kuma tsani. Kasuwanci ta harkar noma kamar sauran harkokin kasuwanci da kadan ko karami ake somawa kafin a mike, sannu a hankali, kamar yadda Hausawa ke cewa “yaro da rararrafe yake tashi”.
Don haka kamfanin da ka kafa ko kuma ‘yar sana’ar da ka soma a harkar noma na bukatar lokacin da zai girma ya kuma habaka, don haka yana da kyau ka yi duba da nazari na yadda yanayin kasuwancin yake, ka tafi sannu a hankali.
Hakuri na daya daga cikin ginshikai a cikin sirrin kasuwanci, hannu da hannu suke tafiya da jajicewa da kuma sha’awa ko kaunar abin da kake yi, domin ga duk namijin da ke son samun nasara a harkarsa ta noma da kuma kasuwanci a wannan fanni sai ya kasance mai hakuri da juriya da kuma jajircewa domin ta hakan ne zai sa ya yanke shawarar a kan abin da ya ga ya dace ba tare da son rai ba, ya kuma tsaya kan shawarwarar da ya dauka da hujja ta hankali da yakini.
Mayar da hankali
Mayar da hankali ta hanyar tsayawa kan abu daya da ka ba shi muhimmanci tare da dagewa a kai yana da matukar muhimmanci ga nasarar kasuwancinka ta fuskar noma.
Shin wannan kasuwanci abin sayarwa ne kamar taki ko irin shuka ko kuma wani aiki ne kamar aikin feshi ko leburanci da ire-iren su?
Koma dai wanne ne a ciki nagartar aikin da kake yi ko abin da kake sayarwa, yana da kyau a matakin farko ka samar da tsayayye ko tabbataccen lokacin bude wurin sana’arka da irin kaya ko aikin da kake yi in har kana so a san ka da wannan.
Muddin za ka yi haka, to za a iya cewa ka dauko hanyar nasara. Ko Bahaushe ya ce, ‘a san mutum a san cinikinsa, in kuma ya bari a san ya daina” wannan shi ne tambarin nagarta.
Aiki tukuru
Hakika “ba a bori da sanyin jiki” in har da gaske za ka yi sana’a ko kasuwancinka da akwai bukatar zage damtse ta hanyar dagewa, a kullum idan ka fito wajen kasuwancinka ko sana’a ka tsara yadda harkar za ta ci-gaba.
Yana da kyau ka rika tambayar kanka shin yaya zan cim ma nasara iri kaza da kaza ko kuma ta yaya zan yi in sauya abu kaza da kawo wa harkarka ci gaba?
Ka dage ka fito da wani tsari ta hanyar yin jadawalin ci-gaban kamfanika ko sana’arka da ko kuwa na yadda za ka motsa daga nan zuwa can ne a shekara.
Idan ka yi haka sai ka dage ka yi a aikace ba wai kawai a tunance ba ko maganance ba, domin mafarkinka ya zama gaskiya, ya tabbata.
Kulla alaka ta sanayya
Kulla alaka ta sanayya zai taimaka maka wajen samun alheri ga sana’arka wanda zai kawo maka ci-gaba da kuma karuwar arziki.
Hakan kuwa zai yi tasiri ko in ce zai taimaka kwarai wajen samun kasuwa da kuma sanin duk wani abin da ke faruwa a harkokinka da kuma bubuwan da ke faruwa dangane da labarin kasuwa da harkar noma.
Kulla mu’amilla da kungiyoyin manoma da sauran kungiyoyin tsimi da tanadi a harakar noma zai taimake ka.
Haka ma sanin kwararru a fannonin aikin noma ta kafofin da yawa na zamani, musamman dandalin sada zumunta.
Yin hakan zai taimaka. Bayan wannan akwai wasu wuraren da za ka nemi sanayya da kulla alaka da wadanda za su taimaka maka wajen samun abokan hulda na cinikayyarka kuma sanin bukatunsu da ma sauran labarun ci gaba da ya danganci harkar noma da sauransu.
Zamani zo mu tafi
A kullum abubuwa na zamani na kara kunno kai a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum, haka ma a harkar noma da kasuwanci ake samun fasahohi na zamani da ke kara saukaka da kuma inganta abubuwa.
Don haka kar ka sake a bar ka a baya a wannan abubuwa na ci-gaba saboda damarmakin da suke sanarwar na kasuwanci.
Don haka yana da kyau ka iya amfani da fasahohin zamani na wayar hannu da samun bayanai a intanet da shafukan sada zumunta da sauransu.
Za su taimaka maka matuka sannan za su saukaka maka rayuwa da kuma harkar kasuwancinka ba kawai ta fanni noma ba