✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 14 da ya kamata ku sani kan tsohon shugaban Chadi, Idriss Deby

Déby ya Jagoranci wata tawaga dake kalubalantar shugaba Hissène Habré a cikin watan Disambar shekarar 1990.

Bayan lashe zaben Shugaban Kasar da aka kammala a makon jiya da kimanin kaso 80 cikin 100, Shugaba Idris Deby na Chadi ya rasu ranar Talata, 11 ga watan Afrilun 2021.

Sanarwar rasuwar shugaban na zuwa ne bayan wata arangama da ya yi da wasu dakarun ‘yan tawayen Arewacin kasar a karshen makon da ya gabata.

“Shugaba Idriss Déby ya rasu a fagen daga yana kokarin fitar da kasar daga yake-yake,” inji Kakakin Rundunar Sojin Kasar, Janaral Azem Bermandoa Agouna, lokacin da yake sanar da rasuwar shugaban.

Marigayi Idris Deby lokacin da ya kawowa Shugaba Buhari ziyara a Abuja

Ga wasu abubuwa da ya kamata ku sani dangane da rayuwa da lokutan marigayi tsohon Shugaban Kasar:

 1.  An haifi Déby ranar 18, ga watan Yunin 1952, a kauyen Berdoba, dake Arewacin Chadi.
 2.  Mahaifinsa talaka ne kuma makiyayi, ya fito daga tsatson kabilar Bidayat dake yankin Zaghawa.
 3. Déby ya zama jagoran mayakan kasar, shekara daya bayan Hissiene Habré ya zama Shugaban Kasa a shekarar 1982, kafin daga bisani a nada shi a matsayin babban kwamanda Rundunar Sojin kasar.
 4. A shekarar 1985, Habré ya tura shi karo karatu zuwa birnin Paris a makarantar École de Guerre; inda ya dawo a shekarar 1986, sannan aka nada shi a matsayin Babban Mai ba da Shawara Kan Tsaron Fadar Shugaban Kasa.
 5. A shekarar 1987, ya jagoranci tawagar sojojin kasar Libya zuwa filin daga, tare da taimakon kasar Faransa a wani yaki da ake kira ‘Yakin Toyota’, inda aka yi amfani da wasu matakai da suka yi sanadiyyar kisan abokan gaba da dama a lokacin.
 6. A yayin gudanar da yakin, ya jagoranci Rundunar Sojin Sama ta Maaten al-Sarra dake Kufrah, a yankin kasar Libya.
 7. Bayan barkewar rikici a ranar daya ga watan Afrilun 1989 tsakanin Habré da Dérby kan karawa dakaru masu tsaron shugaban kasa karfi, Habré ya kalubalanci Déby da Ministan Harkokin Cikin Gida, Mahamat Itno da kwamandan Rundunar Sojin kasar kan yunkurin juyin mulki.
 8. Déby ya jagorancin tawagar soji ta farko zuwa yankin Darfur na kasar Sudan, sai kuma Libya inda Shugaba Gaddafi ya karbe shi a yankin Tripoli, shi kuma Itno da Djamous aka kama su anan aka kuma kashe su.
 9. Dukkansu su ukun ‘yan kabilar Zaghawa ne, Habré ya fara yunkurjn fara wayar da kan jama’a kan kalubalantar kabilarsu.
 10. Déby ya Jagoranci wata tawaga dake kalubalantar shugaba Hissène Habré a cikin watan Disambar shekarar 1990.
 11. Ya yi nasarar lashe zaben Shugaban Kasa a shekarar 1996 da 2001, bayan kuma an kawar da shi daga shugabancin Kasar ya sake samun nasara zama shugaban a shekarar 2006 da 2011 da 2016 da kuma shekarar 2021.
 12. Ya kara sunan “Itno” a sunan Mahaifinsa a cikin watan Janairun 2006.
 13. Ya yi karatu a Cibiyar Juyin-juya Hali ta Duniya ta Muammar Gaddafi a Libya.
 14. An kashe shi a watan Afrilun 2021 yayin da yake ba sojojinsa umarni kan kaiwa ‘yan tawaye farmaki.