A ranar Talata, 19 ga Afrilu, 2022 ake jana’izar Gimbiya Lolowah, ’yar Sarki Fahd na kasar Saudiyya, wadda aka kashe mahaifinta tun tana matashiya.
Ga kadan daga abubuwan da ya kamata ku sani a game da Gimbiyar Lolowah bint Fahd Al Saud, wadda ta rasu tana da shekara 74 a duniya.
- An haife ta a shekarar 1948 a garin Ta’if na kasar Saudiyya,
- Ita ce ta tara a ’ya’yan da Sarki da matarsa Iffat Al Thunayan suka haifa.
- Ta yi karatunta a kasar Switzerland a makarantar Lausanne
- Ta auri dan uwanta na dangi, Saud bin Abdul Muhsin
- ’Ya’yanta uku kuma aurenta ya mutu shekara 10 da ta wuce
- Tana da shekara 27 a duniya aka kashe mahafinta a watan Maris din 1975
- Gimbiya Lolowah, ta kasance mai wayar da kan mata a Saudiyya musamman a fannin ilimi
- Ta yi aiki a matsayin mamba a kwamitin kasuwanci na kasa da kasa da kungiyoyin kasuwanci da masana’antu na Saudiyya
- A 2006 ta jagoranci tawagar ’yan kasuwar Saudiyya zuwa wani babban taro a birnin Hong Kong na kasar China
- Ta halarci tarukan harkokin kasuwancin Saudiyya a kasashen waje, tare da rakiyar manyan ’yan gidan sarautar Saudiyya a tafiye-tafiyen diflomasiyya