✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 10 da suke sa mata su ji suna son namiji

’Yan mata sun bayyana wa Aminiya abubuwa daban-daban da ke birge su

’Yan mata sun bayyana wa Aminiya abubuwa daban-daban da ke birge su, har su ji suna son namiji.

Waddannan abubuwan in ji matan, suna cikin wadanda suke fara kalla har su kai ga jan hankalinsu su amince su fara soyayya da namiji.

Sai dai kamar yadda kowa ke da dabi’u da halayen da suka bambanta shi da wani, to haka yake a gurin ’yan mata ma, kowace akwai abin da take kula da shi a gurin namiji, da zai sa ta so shi.

Aminiya ta tattauna da wasu mata kan abin da namiji zai yi ya burge su har su yi soyaya da shi.

Wata budurwa mai suna Nusaiba, ta bayyana wa Aminiya cewa, “Ni yadda namiji ke tafiya ne abin da ya fi burge ni da shi.”

Ita kuwa wata mai suna Nafisa Bello cewa ta yi, “Yanayin kwalliya da tsarin namiji da kuma yanayin hankalinsa ne suka fi burge ni. Idan namiji na tunani kamar yaro karami duk kwalliyar shi, zan iya barin shi.”

Sai dai ita kuwa wata budurwar mai suna Goodness Auta, ta ce, “Nauyin aljuhun namiji ne zai sa ni son shi, da kuma tsayi da kyawun shi.”

Ga karin wasu abubuwan da matan suka ce sun fi burge su da maza:

 • Tsawo
 • Kyan fuska
 • Kwalliya da sa kaya
 • Natsuwa
 • Kyau
 • Launin fata
 • Diri/Kira
 • Hankali
 • Yanayin kamshin turare
 • Kafa
 • A karshe, ‘yan mata da dama sun bayyana cewa kyau namiji suke kula da a farko.