✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 10 da jawabin Buhari ya tabo a Babban Taron APC

Aminiya ta taurari muku muhimman abubuwa 10 da jawabin Buhari ya tabo

Bayan shafe tsawon lokaci ana ta jeka-dawo, daga karshe dai jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da Babban Taronta na Kasa a ranar Asabar.

Taron, wanda ya gudana a dandalin Eagle Square da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, ya sami halartar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Mataimakinsa, Yemi Osinbajo da Shugabannin Majalisun Dokoki na Tarayya da dukkan Gwamnonin jam’iyyar da ’yan majalisu da ma kusoshinta daga fadin kasar nan.

A yayin da yake gabatar da nasa jawabin, Shugaba Buhari ya tabo batutuwa da dama da suka shafi APC da ma Najeriya baki daya.

Aminiya tatsakuro muku muhimman abubuwa 10 da jawabin Shugaban ya kunsa:

Kwamitin Riko ya farfado da ruhin APC

Buhari ya ce Kwamitin Rikon APC karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya farfado da ruhin jam’iyyar musamman ta bangaren sasanta mutanen da suke rikici da juna a jihohi.

Hakan, a cewarsa, ya kara wa APC karfi a kan wanda take da shi a baya.

Gwamnoni uku sun dawo APC

Bugu da kari, Buhari ya ce daga cikin nasarorin da jam’iyyar ta samu a baya-bayan nan har da yadda Gwamnoni uku masu ci suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa cikinta.

Kazalika, ya ce APC ta kuma karbi Mataimakin Gwamna da Sanatoci da ’Yan Majalisun Tarayya da na Jihohi masu yawan gaske, kari a kan miliyoyin mambobin da suka biyo su cikinta.

Mambobin APC masu rajista yanzu sun haura miliyan 40

Buhari ya nuna jin dadinsa kan yadda ya ce a yanzu haka, bayan kammala rajistar ’yan jam’iyya da Kwamitin Rikon ya yi, yanzu APC na da mambobi miliyan 41.5.

Ya ce hakan ko tantama babu na nuni da cewa APC ce babbar jam’iyya a Najeriya kuma tana da karfi iya lashe kowane irin zabe.

Akwai bukatar hadin kai don tunkarar zaben 2023

Da ya waiwaya bangaren babban zaben 2023 da ke tafe kuwa, Shugaba Buhari ya ce Babban Taron ya zo a lokacin da sauke shirye-shiryen tunkarar kakar zabe mai zuwa.

Ya ce akwai bukatar APC ta dada zama tsintiya madaurinki daya don ganin ta ci gaba da rike madafun iko bayan karewar wa’adinsa.

Rikice-rikicen cikin gida za su iya yi wa APC illa

Shugaban ya ce ko a kwanakin baya sai da ya saka baki a rikicin cikin gidan da yake faruwa a wasu jihohin.

Sai dai ya ce wadannan rikice-rikicen ba sababbin abubuwa ba ne musamman a dimokuradiyya.

Ya roki a ’ya’yan jam’iyyar da su guji kara rura wutar rikicin wanda zai iya fusata wasu.

A fita a yanki rajistar zabe

Buhari ya kuma hori mambobin jam’iyyar da kada su yi kasa a gwiwa wajen sabunta rajistar zabensu.

Ya ce hakan na da muhimmanci saboda shi ne zai nuna wa duniya cewa ƴaƴansu ba na taron tsintsiya ba shara ba ne, yana mai cewa in ba su fito ba, yawansu zama mara amfani.

A guji Yi Wa Jam’iyya Zagon Kasa

Ya ce dole su guji yi wa jam’iyya zagon kasa, idan bukatarsu ta samun takara ta gaza kai wa ga gaci.

Ya shawarce su da su yi aiki tare ta hanyar fifita bukatun jam’iyya a kan na kashin kansu.

A guji kakaba ’yan takara

Shugaban ya kuma yi gargadi kan kakaba ’yan takarar da mutane ba sa so, inda ya ce a 2023, dole ne a ba ’yan takarar da mutane suka fi so.

Ya kuma ja hankalin sabbin jam’iyyar da su guji siyasar kudi sannan su ba dukkan ’yan takara damar da ta dace, ta hanyar samar da dimokuradiyyar cikin gida.

Sabuwar Dokar Zabe za ta sauya fasalin zabe a Najeriya

Game da sabuwar Dokar Zaben da ya sanya wa hannu a kwanakin baya kuwa, Buhari ya ce yana fatan za ta inganta harkokin gudanar da zabe a Najeriya ta kuma tabbatar da adalci.

Ya shawarci dukkan jam’iyyu da su yi la’akari da tanade-tanaden sabuwar dokar, saboda ta zame musu jagora a kan kowanne matakin da za su dauka.

Makomar Najeriya na hannun Daliget-daliget

Buhari ya tunatar da wakilan jam’iyyar, wato daliget-daliget cewa su suke da wuka da nama wajen zaben ’yan takara ga jam’iyyar, don haka makomar Najeriya na hannunsu, wajen zaba mata shugabanni na gari.

Ya ce ya zama wajibi su zabi ’yan takara jajirtattu, marasa son kai, kuma masu rikon amana.