Ranar Laraba da kusan karfe 11.30 Farfesa Ibrahim Gambari ya isa Fadar Shugaban Kasar Najeriya, inda za a gudanar da taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya.
Kwana guda kafin nan dai kafofin yada labarai sun yi ta yada cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin sabon Shugaban Ma’aikata.
Ana daf da fara taron, Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya sanar da hakan a hukumance, kuma Farfesa Gambari ya je ya zauna a kujerar da marigayi Malam Abba Kyari ke zama lokacin yana raye.
Shin wane ne Farfesa Ibrahim Agboola Gambari?
Ga wasu muhimman abubuwa 10 game da mai yiwuwa ba ku sani ba game da sabon Shugaban Ma’aikatan:
- An haifi Ibrahim Gambari a ranar 24 ga watan Nuwamba, 1944, a Ilori, babban birnin jihar Kwara, Najeriya.
- Ibrahim Gambari ya yi karatun sakandare a King’s College da ke Legas. Ya yi digirinsa na farko a London School of Economics, wadda ya kammala a 1968 kuma ya samu shaidar kwarewa a fannin harkokin kasashen waje.
- Ya yi karatun digirinsa na biyu (M.A.) a shekarar 1970 daga nan ya yi digiri na uku (PhD) a shekarar 1974 a Jami’ar Columbia ta birnin New York da ke Amurka inda ya samu shaidar kwarewa a fannin kimiyyar siyasa da fannin harkokin kasashen waje.
- Daga nan sai Farfesa Gambari ya koma fannin karantarwa inda ya koyar daga shekarar 1969 a jami’ar City University ta jihar New York a Amurka. Daga bisani kuma ya yi aiki da Jami’ar Albany, sannan sai Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a jihar Kaduna inda ya koyar daga 1977 zuwa 1980.
- Daga shekarar 1984 zuwa 1985 Ibrahim Gambari ya zamo ministan harkokin wajen Najeriya.
- Daga shekarar 1986 zuwa 1989, Farfesa Ibrahim Gambari ya yi aiki da jami’o’i uku a birnin Washington, D.C. na Amurka wadanda suka hada da: Johns Hopkins School of Advanced International Studies, da Jami’ar Georgetown da kuma Jami’ar Howard.
- A ranar 1 ga watan Janairun 2010 Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya da Shugabar Kungiyar Tarayyar Afirka suka nada Farfesa Gambari a matsayin Wakilin Hadin Gwiwa na Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka a Yunkurin Warware Rikicin Yankin Darfur.
- Farfesa Gambari ya zamo shugaban Jami’ar Jihar Kwara na farko a 2013, bayan da Gwamna AbdulFatah Ahmad ya nada shi.
- A lokacin yana Ministan Harkokin Waje ya ba da gagarumar gudunmawa wajen kwantar da kurar da ta taso sakamakon yunkurin fasa-kwaurin Mallam Umaru Dikko daga Birtaniya lokacin mulkin soji na Buhari.
- Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya karrama Farfesa Gambari da lambar yabo mafi daraja da ake bai wa wadanda ba ‘yan kasa ba a 2012.