Da gaske ne shan abu mai tsami da mai gas a mace mai neman haihuwa yana iya hana ta daukar ciki?
Amsa: A’a, a likitance babu kanshin gaskiya a wannan batu. Hasali ma, a dan binciken da na yi miki, cewa aka yi mace mai son ta dauki ciki da wuri ta guji shaye-shayen ganyen shayi da kofi da yawa. Sa’annan ta guji busa hayakin taba sigari da ruwan barasa da magunguna barkatai wadanda ba ma’aikacin lafiya ne ya rubuta su ba.
Kai ko da ma ma’aikacin lafiya ne zai rubuta, yana da kyau mace mai son daukar ciki ta tambaye su ko ba zai hana daukar ciki ba. Wadannan duk za su iya hana mace mai neman juna biyu samun rabo. Kai ban da hana daukar cikin ma ko ta samu, za su iya sa a yi bari. Amma fa kada a ga mai tu’ammali da wadannan abubuwa ta samu juna biyu a ce ba haka ba. A’a, su wadannan rage yiwuwar samun cikin suke.
Ni kuma duk cikin da na samu sai na yi ta laulayi na tsawon watanni uku ko hudu, kuma alhali ina da ’ya’ya, ba shi ne cikina na farko ba. Ko ina da matsala ke nan a mahaifa?
Daga Mema, Daura
Amsa: E, duk da yake an fi samun laulayin ciki a amarya, ba dole ne a ce sai amaryar ce kawai za ta yi laulayi ba, har manyan mata ma kan yi irin wannan laulayi. Sai dai kawai abin ya fi kamari ne a amarya fiye da wadda ta sha haihuwa. Su ma a amaren jiki-jiki ne, ba kowace ba ce ke samun matsalar. Tun da laulayin na tafiya bayan watanni uku zuwa hudu, kusan a iya cewa ba matsala. Da kamar baya ragawa ne har karshen watanni taran, shi ne za a ce sai an bincika lafiyar mahaifar.
Duk haihuwar da nake ina haifar yara bulbul, amma da sun kai wasu watanni sai su fara rama duk da ina sa ba su abincin gwangwani daga watanni 6. Sai bayan an yaye su suke kiba. Me ke sa haka?
Daga Maman Ruzaina, Jigawa
Amsa: In dai a wannan lokacin ramar ba su yawan laulayi na gudawa da yawan mura da tari da zazzabi, to ba abin damuwa ba ne. A lokacin da yara kan girma wasu sai sun zabge dama kafin su dawo su yi jiki. Idan kina kai su allurar riga-kafi a kai-a kai, a jikin katin akwai inda ake zana girman yaron, idan akwai matsala ma’aikatan za su fada.