✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin misali daga rayuwar Sa’adu bin Abu Wakkas (3)

Umar bin Khaddabi (RA) ya taba tambayar wani ma’abucin hikima a cikin Larabawa ana ce da shi Amr bin Mas’ud bin Yakrib ra’ayinsa a kan…

Umar bin Khaddabi (RA) ya taba tambayar wani ma’abucin hikima a cikin Larabawa ana ce da shi Amr bin Mas’ud bin Yakrib ra’ayinsa a kan Sa’adu bin Abu Wakkas (RA)? 

Sai Amr ya ce, ai Sa’adu (RA) mutum ne mai saukin kai da sanin ya kamata. Ga shi dai Balarabe a yanayin tufafinsa amma a zuci tamkar zaki ne, Sa’adu mutum ne mai adalci, yakan yi rabo daidai a tsakanin Musulmi, kuma ga shi da tausayi. Lokacin Yakin Badar, Sa’adu ya kashe Sa’id bin Al-As, kuma ya dauke takokbinsa. Da Manzon Allah (SAW) ya samu labari, sai ya umarci Sa’adu (RA) ya mayar da wannan takobi tare da sauran ganimar da ya dauka. Nan da nan Sa’adu ya bi umarnin Manzon Allah (SAW). To amma bayan wani dan lokaci sai ga Mala’ika Jibrilu (AS) ya sauko da wahayi cikin Suratul Anfal, Allah Ya umarci Manzon Allah (SAW) da ya kyale Musulmi su ci moriyar abin da suka samu a filin yaki. Saboda haka sai Annabi (SAW) ya umarci Sa’adu (RA) ya dauki takobinsa.

A lokacin da fitina ta tashi a zamanin halifancin Amirul Muminina Usman bin Affan (RA), har ta kai ga kashe Sayyidina Usman (RA), sai Sa’adu ya janye jikinsa ya kame daga shiga kowane bangare. Wata rana dansa Umar ya ziyarce shi a inda yak ebe kansa, lokacin da ya hango dansa, sai Sa’adu (RA) ya ce: “Ya Allah! Ina neman tsarinKa daga wannan mutum (mai zuwa wurina). Da dansa Umar ya iso gare shi, sai ya ce masa: “Ya Babana! Yanzu kana ganin Musulmi suna fada da ’yan uwansu Musulmi kai kuma kana nan?” Sai Sa’adu (RA) ya ce: “Ka yi min shiru domin na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa Allah Yana son Musulmi mai tsoron Allah, mai kaucewa daga (shiga) fitintinu.”

Sa’adu (RA) ya rayu rayuwa mai tsawo kuma ya kusanci halifofin Manzon Allah (SAW) guda hudu, kuma ya rayu a bayansu.

A takaice ga yadda rayuwarsa ta kasance a zamanin Annabi (SAW) da zamanin halifofinsa:  

 

Rayuwar Sa’adu a lokacin Manzon Allah (SAW):

Sa’adu (RA) yana da matsayi mai girma a tarihin Musulunci, ya nuna jarumta a fagagen yake-yaken da ya halarta tare da Manzon Allah (SAW). sun tsaya  

 

Rayuwar Sa’ad a lokacin Manzon Allah (SAW):

 Sa’adu (RA) yana da matsayi mai girma a tarihin Musulunci, domin ya nuna jarumta a fagagen yake-yaken da ya halarta tare da Manzon Allah (SAW) da wadanda suka biyo baya kamar yadda za mu gani a nan gaba. Sa’adu ne mutum na farko da ya fara zubar da jinin wani kafiri domin kare Musulunci. Yadda abin ya faru kuwa shi ne wata rana Sa’adu da Ammar bin Yasir da Sa’idu bin Zaid da Abdullahi dan Mas’ud (RA), a hanyarsu ta zuwa Makka, sai suka tsaya domin yin Sallah. Da ayarin kafiran Makka irin su Abu Sufyan da Akhmas bin Sharnak da Abdullahi bin Aktal suka ga Musulmi suna yin Sallah, sai suka fara yi musu isgili da zagi cikin tozartawa da wulakanci. A wannan hali, Abdullahi bin Aktal ne ya fi zakewa, domin har ya yi yunkurin cutar da wani daga cikin ayarin Musulmi da suke Sallah. A nan ne Sa’adu ya kasa daurewa ya rarumi wani kashi da ke bayansa ya jefi Abdullahi bin Aktal da shi, kuma ya yi masa rauni. Wannan shi ne ya sa ya zama Musulmi na farko da ya fitar da jinin wani kafiri don kare martabar Musulunci. Haka kuma wata rana Sa’adu (RA) ya shiga ayarin Ubaidah bin Haris don leko abokan gaba, sai suka ci karo da wani gungun kafirai wadanda suka nuna musu muguwar adawa. Sa’adu (RA) ya kalubalance su kuma ya dana kibiya a bakarsa ya harba cikin taron wadannan kafirai, don haka ne ake cewa Sa’adu (RA) ne Musulmi na farko da ya fara harbi a cikin abokan gaba don kishin Musulunci.

Uwar Muminai A’isha (RA) ta ruwaito cewa, lokacin da Manzon Allah (SAW) ya isa Madina a kwanakinsa na farko ya dauki lokaci ba ya iya yin barci da wuri, tamkar dai yana wata barazana a gare shi. Wta rana sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ina ma wani sahabina zai zo nan a wannan dare domin yin gadina!” Sai suka ji motsin makamai a kusa da su, Manzon Allah (SAW) ya tambayi dalilin wannan motsin, sai aka shaida masa cewa ai Sa’adu dan Abu Wakkas ne. Da Manzon Allah (SAW) ya tambaye shi dalilin zuwansa da makamai a cikin wannan dare, sai Sa’adu (RA) ya ce, ya zo ne domin ya yi gadi, gudun kada a samu wata barazana ga rayuwar Annabi (SAW). A nan sai Manzon Allah (SAW) ya yi masa addu’a, sannan ya je ya yi barci.

 

Sa’adu a lokacin Yakin Badar:

Sa’adu (RA) ya nuna matukar jarumtaka da son kare addini a filin daga a lokacin Yakin Badar. Abdullahi dan Mas’ud (RA) ya ce, “Na ga Sa’adu dan Abu Wakkas (RA) a filin fama (lokacin Yakin Badar) yana yaki cikin jarumta (da nuna kwarewa).” Ya kara da cewa: “Mun halarci filin yaki ni da Sa’adu (RA) da Ammar bin Yasir, cikin yarjejeniyar raba ganima a tsakaninmu, sai Sa’adu ya samu fursunonin yaki guda biyu, mu kuma muka samo daidaya.” A wannan ran ace Sa’adu (RA) ya yi ta harbin kafirai yana addu’a yana harbi, Annabi (SAW) yana yi masa addu’a har lokaci mai tsawo. Sa’adu yana harbi yana fadin: “Allahumma zalzil akadamuhum, war’uf kulubihim waf’al bihim…. har zuwa karshe.” Annabi (SAW) kuma yana cewa: “Allahumma istajib li’sa’adin.” (Ma’ana: Ya Ubangiji Ka girgiza (raunana) duga-dugansu, Ka jefa tsoro a zukatansu, Ka yi musu kaza da kaza…” Annabi kuma yana cewa: “Allah Ka amsa wa Sa’adu.) dabarani ya ruwaito.  Haka Sa’adu (RA) ya rika wannan addu’a yana harbin kafirai, (Allah Ya kara masa yarda.)

 

Sa’adu a Yakin Uhudu:

Sa’adu (RA) ya tsaya tare da Manzon Allah (SAW) a rana Yakin Uhudu yana ba shi kariya cikin jarumta da nuna kwarewar yaki. Ya yi fama da kafirai, a wannan rana ma yana addu’a yana harbi da kibiya a cikin makiya Allah.  Annabi (SAW) kuma yana taya shi da wannan addu’a yana kuma yi masa fatan Allah Ya amshi addu’o’insa. Lokacin da yaki ya yi tsanani, sai Annabi (SAW) ya rika bai wa Sa’adu umarni da kansa, yana cewa “Jefa kibiyarka ya Sa’adu nab a ka fansar mahaifina da mahaifiyata.” Amirul Muminina Aliyu dan Abu dalib (RA) ya ce: “Babu wanda Manzon Allah (SAW) ya yi wa irin wannan magana face Sa’adu.” Buhari ya ruwaito, amma wadansu malaman tarihi sun tabbatar da cewa Annabi (SAW) ya yi irin wannan addu’a (magana) ga Zubair bin Awwam. (Tirmizi ya ruwaito a Sunaninsa: Hadisi na 2943).

Kuma a lokacin da ake tsakiyar Yakin Uhudu, sai Sa’adu ya lura Malik dan Zubair yana ta yin barna wajen kashe Musulmi da raunata su, sai Sa’adu (RA) ya lalabo ya kashe shi ta hanyar harbi da kibiya.

Sa’adu a Yakin Banu kuraiza

A lokacin Yakin Banu kuraiza ma Sa’adu (RA) ya yi matukar nuna jarumta da iya yaki. Sa’adu ya nuna hikima da rashin tsoro ta hanyar razana kafirai da ’yantar da Musulmi. 

A yakin Hunain, Sa’adu ne yake dauke da tutar Muhajirai, ya tsaya tare da Manzon Allah (SAW) a lokacin da wadansu mutane suka shiga halin tsoro har ma suka gudu daga fagen daga. A takaice dai Sa’adu (RA) ya kasance tare da Manzon Allah (SAW) tun farkon Musulunci yana mai kokarin kare Musulunci har Manzon Allah (SAW) ya yi wafati. 

Za a iya samun Ustaz Aliyu Gamawa ta tarho: 08023893141, 08035829071.