Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce abin kunya ne Najeriya ta ci gaba da shigo da albarkatun man fetur daga ketare duk da kasancewarta daya daga cikin manyan masu samar da shi a duniya.
Ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a garin Ewohimi da ke karamar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas da ke jihar, yayin taron shekara 10 da tunawa da Cif Jeremiah Ighodalo, mahaifin shugaban bankin Sterling, Dokta Asue Ighodalo.
- Kotu ta sa a tsare Bakanuwar da ake zargi da kisan jikanta
- ‘Najeriya na fuskantar barazanar tsaro mafi girma tun bayan Yakin Basasa’
Gwamnan ya ce, “Ci gaba da shigo da mai Najeriya babban abin kunya ne ga kasar.
“A matsayinta na ja-gaba wajen samar da danyen man a nahiyar Afirka, bai cancanci a ce Najeriya na shigo da mai daga waje ba. Gaskiya abin kunya ne a ce har yanzu muna shigo da shi.
“A matsayinmu na kasa a daidai wannan lokacin abin kunya ne babba ci gaba da shigo da man,” inji Gwamna Obaseki.
Shi ma da yake nasa jawabin kan matatar man da yake ginawa, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce yana fatan a cikin shekarar 2023 za ta fara aiki gadan-gadan.
Ya ce matatar za ta samar da man da ilahirin Najeriya da ma makwabtan kasashe za su rika amfani da shi.