Tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Ishaya Bamaiyi (mai ritaya) ya ce yanzu ne al’ummar Najeriya suka san sun zabi shugaba na kwarai, ba wadanda aka dora musu ba.
Janar Ishaya Bamaiyi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa garin Zuru a Jihar Kebbi, inda ya ce, yanzu ne al’ummar Najeriya za su amfana da dimbin arzikin da kasar nan ke da shi, sakamakon zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran shugabanni a matakai daban-daban da suka yi.
Janar Bamaiyi ya ce a nasa hasashen yanzu ne Najeriya za ta samu ribar dimokuradiyya cikin adalci da kyautata wa al’umma musamman ganin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke da hangen nesa da kuma gaskiya a cikin al’amuransa.
Ya ce ’yan Najeriya za su yi murna da godiya ga Allah saboda samun jagora adali mai fada da cikawa, “Kuma abin da ya rage shi ne mu yi ta yi wa shugabanninmu addu’o’in samun jagoranci daga Allah,” inji shi.
Janar Bamaiyi ya ce, kada jama’a su zaci cewa dadi zai zo cikin kankanen lokaci, “Yanzu ne ’yan Najeriya ke da jan-aiki a gabansu, ganin shekarun da aka kwashe ana almubazzaranci da dukiyar al’umma,” inji shi.
Ya ce yana da tabbacin duk da cewa Shugaba Muhammadu Buhari yana mulki ne a tafarkin dimokuradiyya, ya hakikance cewa zai yi kokarin tabbatar da adalci tare da ba kowa hakkinsa.
“Na tabbata yadda na san halin Muhammadu Buhari in dai Buhari nan ne da na sani har yanzu, to na yi imani duk wanda ya kwashe kudin kasar nan ko yake da hannu a cikin hakan zai sa a maido su a yi wa jama’a aiki, domin azzalumi ba ya kusantarsa, koda dan uwansa ne kuwa. Buhari ba tara abin duniya ya dame shi ba, illa al’ummar kasa da kasar yake so, kuma kowa ya san haka. Ire-irensu ba su da yawa a cikin kowace kasa a duniya,” inji Janar Bamaiyi.
Abin duniya bai damu Buhari ba – Janar Bamaiyi
Tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Ishaya Bamaiyi (mai ritaya) ya ce yanzu ne al’ummar Najeriya suka san sun zabi shugaba na kwarai, ba wadanda…