Zee (mun kira ta da wannan suna saboda ta nemi mu boye sunanta) matar aure ce mai shekara 26 wadda muka iske ta caba ado tana karkada makullin motarta kirar Venza.
“Mutumin nan (mijinta) da ake cewa sa’an mahaifina ne, ya yi min duk abin da saurayi ba zai iya yi min ba kuma har cikin zuciyata ina son shi.
- Yadda za ki zama cikin matan da mazan yanzu ke so
- Soja ya kashe yaro saboda mangoro a Kaduna
- Yadda za ki sa namiji ya nutse cikin kaunar ki
“Kafin na aure shi, ni da saurayina mun kasance cikin tsananin kaunar juna ta tsawon shekaru amma a bayyane yake cewa bai shirya ba; da mijina kuma ya bayyana dole na rabu da shi”, inji Zee.
A tsawon rayuwata, daga yankin Arewaci da Kuduancin Najeriya na san ’yan mata da yawa wadanda ke auren, ko suke burin auren, maza sa’annin ubanninsu.
Aminiya ta tattauna da wasu matan da suka nemi a sakaya sunayensu, suka kuma bayyana mata dalilansu na zabar auren maza masu aure.
Hakika samun wanda kake so da kuma rayuwa da shi na cikin abubuwa mafiya faranta rai. Da ma an ce babu ruwan so da tsufa ko yarinta….
Ga dalilan matan da muka zanta da su na auren mazajensu:
‘Kama kasa’
Duk mace na bukatar kwanciyar hankali; ta samu mijin da zai ba ta cikakkiyar kulawa, ya biya mata bukatun yau da kullum da kuma tabbacin dorewar wadata ta bangaren kudi.
Zee ta ce mazan da suka manyanta sun riga sun kafu, aljihunsu ya yi nauyi, sabanin samari ’yan shekaru ashirin da wani abu wadanda yanzu suke neman yadda za su gina rayuwarsu.
Matashiyar ta kara da cewa ta gwammace auren tsoho ‘wanda ya kafu’ da fadi-tashi a kan matashin da ke neman yadda zai ‘tsaya da kafafunsa’.
“Mijina ya riga ya yi shekaru yana aiki kuma ya kafu; ni abin da ya rage min kawai shi ne in more rayuwa cikin walwala.
“Amma ni da tsohon saurayina duk kanwar ja ce, kowannenmu kokari yake ya samu inda zai dosa a rayuwa”.
Hankali da gogewa
’Yan magana kan ce, ‘Abin da babba ya hango, yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba’.
Wata mata mai shekara 28 wacce za mu kira Bunmi ta ce maza da suka manyanta sun fi fahimtar rayuwa da lakantar zamantakewa.
Ta ce sabanin matasa, dattawa na da gogewa a rayuwa saboda a baya sun shiga yanayi iri-iri, sun yi kura-kurai kuma sun koyi darussa daga hakan.
A cewarta, bayan haka, mazan da suka manyanta sun fi kwarewa ta bangaren jima’i.
Ta ce, “A baya sun yi alaka da wasu mata kafin ke, sun samu gogewa kan yadda za su gudanar da alaka mai kyau.
“Sun kuma fi kwarewa wajen kwanciyar aure saboda sun dade suna yi, sun lakanci yadda za su gamsar da mace.”
Ta kara da cewa wasu matan sun fi son mazan da suka manyanta ne saboda tunanin cewa za su gamsar da su saboda karfin jima’insu.
Sadarwa
Sadarwa na da muhimanci a duk abin da muke yi na rayuwa!
Mata na matukar son su ga namiji yana mai da hankalinsa gare su yana sauraren su.
Esther, mai shekara 27, ta bayyana cewa maza da suka manyanta ba su da lokacin yin gaba ko jira sai mace ta kira su.
“Mazan da suka manyanta ba su da lokacin kananan maganganu cewa ‘in ba ta kira ni ba, ni ma ba zan kira ta ba’.
“Su kaifi daya ne; sukan kuma yi magana ne a kan abubuwa yadda ya kamata kai tsaye babu kauce-kauce,” inji ta.
Amincewa
“Namiji mai yawan shekaru ya yarda ya aure ki duk yadda kike, ba tare da damuwa da dirinki ko wani abu ba; shi nagartarki yake nema ba fasalin jikinki da kike yi wa ciko ba.
“Zai yaba miki a yadda kike tare da kokari a koyaushe don ganin kin samu ci gaba, ba wai ya sauya ki ba,” inji Esther.
Gasa
Zee ta ce, “Kamar yadda na fada, shi dattijo ya riga ya kafu, so yake yi ki zo ki huta, ba gasa yake da ke ba – ta ina ma za ki fara ke ’yar shekaru ashirin?”
Kulawa da tarairaya
Ita ma wata matar da za mu kira da suna Chika ta ce mata da yawa sun fi son maza masu aure saboda sun fi nuna kulawa da mutunta mace da kuma ba da hakkin aure.
“Za su ba ki kulawa su lallashe ki kamar karamar yarinya; ban ce matasa ba sa yi ba, amma mazan da suka manyanta sun fi yi.”
Shin akwai wasu dalilai kuma da kuke ganin na sa ’yan mata su zabi auren maza masu aure? Kuna iya bayyana ra’ayinku ta hanyar yin tsokaci ko a shafukanmu na sada zumunta.