Domin sauke shirin latsa nan
Tashe-tashen hankula sun zama tamkar jamfa a Jos a Najeriya – ana kokarin shawo kan wannan, sai wani ya barke a wani wuri.
A Karamar Hukumar Jos ta Arewa ta jihar Filato ana cikin kokarin kwantar da kurar da ta taso sakamakon kisan wasu matafiya, sai ga wasu sun kai hari a kan wata al’umma inda suka kashe mutane suka kona gidaje.
Shin babu hanyar kawo karshen wadannan rikice-rikice ne?