✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa na yanke mazakutar mijina

Matar auren da ta sa wuka ta yanke mazakutar mijinta ta ce kwaya ta sa masa ya yi barci sannan ta samu damar yanke masa…

Matar auren da ta sa wuka ta yanke mazakutar mijinta ta ce kwaya ta sa masa ya yi barci sannan ta samu damar yanke masa al’aura.

Da yake gabatar da matar mai shekara 20, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal ya ce matar ta yanke al’auranr mijinta ne bayan sa-in-sa da suka samu kafin ranar da abin ya faru a ranar 1 ga watan Yuli.

Matar mai dauke da tsohon ciki wadda ta bayyana nadama game da abin, ta ce zafin rai da shaidan ne suka sa ta aikata.

Da take yi wa ‘yan jarida bayani, matar ta ce fushin nata ya samo asali ne daga zargin mijin nata da neman mata, kuma sun dade suna rikici ana kokarin sasanta su a auren nasa mai shekara 10 ba tare da samun nasara ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ya ce rundunar za ta gurfanar da matar ‘yar garin Tella na karamar hukumar Gassol, a kotu bisa zargin yunkurin aikata kisa.