Aminiya ta tattauna da wani matashin da ya kammala karatun sakandare, amma yake da fasahar kere-kere – inda kawo yanzu ya kera jirgi maras matuki wanda yake tashi sararin samaniya da ma wasu ababuwan fasahar na daban. Ya bayyana yadda ya hada jirgin da kuma abinda ke sa ya yi shawagi.
Mene ne takaitaccen tarihinka?
Sunana Shamsudeen Jibril, ina zaune a Unguwar Kawo a Kaduna. Amma asalina dan garin Bagaldi ne da ke Karamar Hukumar Soba a Jihar Kaduna.
A bana na kammala karatuna a Kwalejin Tunawa da Sardauna (SMC) da ke Unguwar Dosa, Kaduna. Na rubuta jarrabawar gama sakandare dina da sakamako mai kyau sosai.
Yaushe kuma yaya aka yi ka fara kere-kere?
Na fara aikin tun ina makaranta lokacin ina zangon karatu na farko a aji biyar. A lokacin malamarmu ta ce kowa ya je ya hada wani abu na fasaha.
Daga nan sai abokina ya fara hada mota, ni kuma na ce zan kera jirgi wanda zai tashi. Na fara hada shi da gora da kwali. Kullum zan ina tunani yaya zan hada abin ya tashi – wallahi har mafarki nake yi – na kera shi ya kuma tashi. Na yi ta samun gora da kwali ina yayyankawa irin fasalin jirgi. Ina yanka fiffiken jirgi da fanka, sai na samu DC Motor na DBD, wanda zai sa shi ya juya, sai na sa batur na hada da shi. A lokacin ina kokarin hada shi ya tashi. Kullum in na tashi bayan Sallar Asuba, zan fara hadawa, yana juyawa. Wadansu daga cikin gidanmu suna cewa wannan wane irin shirme ne. Amma in na kai makaranta sai malamai da abokai su yaba mini cewa na yi kokari.
Wani abokina ya ce in je Cibiyar Kere-Kere ta Sojin Sama (Airforce Institute of Technology), Kaduna domin koyo wasu abubuwa kan yadda jirgin zai tashi. Na samu malamarmu mai suna A’isha na sanar mata ina son zuwa makarantar sojin sama domin karo ilimi kan abin. Ta kai ni wajen Firansifal ya rubuta mini takardar gabatarwa zuwa cibiyar sojin saman. Da na kai musu takardar da kuma abin da nake yi sai suka fara koya mini tare da abokina karatun yadda yadda jirgi yake. Akwai wata Laftanar Jirgin Sama, wato Flight Lieutenant Ofodile Anulika ta taimaka mana sosai. Daga nan sai muka fara kerawa, ashe akwai wasu bangarori da ya kamata mu sani, na yadda elebetor da aileron da fiffike ke aiki a jirgi. Sai muka fara hada namu wanda ba matuki a cikinsa. Alhamdulillah ga shi yanzu mun kera ya kuma tashi.
Wadanne ababuwa ka kera zuwa yanzu?
Na kera abubuwa da dama. Kamar detector da helicopter da aeroplane.
Me ka yi amfani da shi wajen kera jirgin?
Na yi amfani da burodin kaji wato farin soson nan da ake kawo rediyo da wasu na’urori a cikinsa.
Ka taba samun tallafi daga wani?
Na samu tallafi daga Flight Lieutenant Nkemdilm Anulika Ofodile, ita ce wacce take tallafa mini da wasu abubuwa sosai.
Wane tallafi kake bukata?
Ina bukatar tallafi sosai saboda ina son ci gaba da karatuna, in karo ilimi a kan kere-kere.
Me kake muradin zama nan gaba?
Ina son zama a Injiniyan Jiragen Sama (Aeronautical Engineer), daga nan sai in zama matukin jiragen sama.
Yaya jirgin yake tashi?
Yadda jirgin ke aiki shi ne; da farko akwai abubuwa a jikinsa sosai kamar su elebator da rudder da ailerons da fanka da kuma batir.
Yadda yake aiki shi ne, akwai fiffiken jirgin. A fiffiken akwai inda iska ke wucewa shi ne aerodynamic da kuma aerofoil shape yadda za ka yanka abu iska ta wuce. A fiffiken akwai iska ta sama sosai, amma ba pressure sosai. Sai dai kuma a kasa akwai iska sosai, amma akwai pressure sosai shi ke sa jirgin ya tashi. Bayan nan akwai four forces da ke aiki a jirgi har ya tashi.
Kamar haka: 1. Trusth. Fanka shi ne thrusth, saboda shi ke jan jirgin.
2. Weight. Shi ne nauyin jirgin. Ya kamata jirgi ya zama tsakiya – bayansa bai yi nauyi ba haka gabansa ma kada ya yi nauyi. Kuma za ka yi amfani da abin da ba ya da nauyi.
3. Lift. Shi ne tashin jirgin. Za ka yi amfani da transmitter da receiber saboda su ne za su rika aika sako zuwa receiber sai ya fara aiki.
4. Drag. Shi ne aerodynamic force.
Bayan nan maganar sarrafawa (control) akwai transmitter da receiber. Transmitter shi ne na’urar sarrafawa. Shi kuma receiber yana cikin jirgin shi ne ke amsar sako daga remote. Amma sai an yi programming nasa a Arduino JabaScript software.
Me ya sa kake sha’awar kera jirgi?
Saboda ina so in ga kasarmu ta ci gaba irin wasu kasashen – mu rika hada jirage namu a kasarmu, maimakon zuwa wasu kasashen muna sayo jirage. Kuma in Allah Ya yarda Najeriya za mu fara kera jiragenmu da kanmu.
Mene ne kiranka ga gwamnati domin dafa wa ire-irenku?
Da a ce gwamnati za ta rika tallafa wa ire iranmu, to kuwa da kasarmu ta ci gaba a fannin kere-kere. Kuma muna kira ga gwamnati ta rika tallafa wa ire-irenmu domin ci gaban kasarmu.
Me yasa ka kera jirgi marar matuki?
Dalili shi ne domin amfanin manoma wajen zuba maganin feshi a gonakinsu da kuma taimakawa wajen inganta sha’anin tsaro a kasarmu.
Ko akwai wata hukuma da ta taba tuntubarka, bayan kera jirgin?
Babu. Sai dai wata kungiya mai suna NASAC da Alhaji Yahya yake shugabanta na fanteka Kaduna, shi ne wanda ya tuntube ni kan jirgin da na yi, kuma yana dafa mini sosai shi ma.