✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na fice daga APC – Haruna Sa’eed

Tsohon wanda ya nemi tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kaduna kuma jigo a Jam’iyyar APC a jihar, Alhaji Haruna Sa’eed ya bayyana cewa ya fice daga…

Tsohon wanda ya nemi tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kaduna kuma jigo a Jam’iyyar APC a jihar, Alhaji Haruna Sa’eed ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar ce saboda rashin shugabanci da rashin daukarsa da mutanensa da muhimmanci. Haruna Sa’eed wanda shi ne dan takarar Gwamna a Jam’iyyar CPC a zaben 2011, ya ce rashin shugabanci da kuma daukarsa da mutanensa da duk da kokarin da suka yi wajen kafa Jam’iyyar APC har ta kafa mulki akwai wadanda ba sa kallonsa da ga shi domin ko gayyatarsa taron jam’iyyar ba a yi. Ya ce ko ba komai a matsayinsa na wanda ya taba rike tutar Jam’iyyar CPC har suka ci zabe amma Jam’iyyar PDP mai mulki ta murde zaben, to ya dace idan ya ba da shawara a Jam’iyyar ta APC a rika dauka sannan kuma a rika damawa da shi.

Ya kuma bayyana wa Aminiya hankan ne a zantarwasu a Kaduna. Haruna Sa’eed ya kara da cewa akwai babban aiki a gaban kwamitin sasanta rikicin APC da ke karkashin Cif Bola Ahmed Tinubu domin a cewarsa an bar shiri tun baya. “Akwai dalilai masu yawa da suka faru har na bar jam’iyyar amma da farko  ina cikin wadanda suka gina wannan jam’iyya ta APC domin jami’yyu ne suka yi hadaka har suka samar da ita APC. Jam’iyyun kuma su ne CPC da ACN da ANPP sannan aka samu ta wasu daga PDP da kuma wani sashe na APGA. An yi haka ne domin an fahimci hannu daya ba ya daukar jinka,” inji shi. “Sai aka ga zai fi dacewa a hada karfi domin a kawar da jam’iyya mai mulki a lokacin wato PDP. Mun yi haka, kuma aiki ya yi kyau har aka samu nasara. Ni a Jihar Kaduna na zo na hada dukan jam’iyyun nan domin mu ga yadda za a yi a tafi tare. Babu karamar hukumar da ban je fiye da sau biyu domin ganin an wayar wa da jama’a kai a yi APC ba. Amma sai ga shi yawancinmu da muka taimaka wajen ganin an kafa jam’iyyar an yi watsi da mu ba a ko kallonmu a matsayin ’ya’yan jam’iyyar. Duk abin da za mu fadi ko muka fadi a kan ci gaban jam’iyya ba a daukarsa da muhinmanci,” inji shi.  

Ya ce, “Ni kuma ina ganin jam’iyya kamata ya yi ta zama waje ne da kowa za a saurare shi. A yanzu haka rikice-rikice sun yi yawa cikin jam’iyyar musamman rikicin shugabanci a Jihar Kaduna. Babu shugabanni a jam’iyyar kuma babu wani shirin da ake yi domin cike gurbin mukaman da ke cikin jam’iyyar duk wadannan da sauran wasu dalilai suka sa na ga zai fi kyau in fice daga jam’iyyar.”