’Yan bindigar da ke cin karensu ba babbaka a tsakanin Jihohin Sakkwato da Zamfara sun dauki alhakin kai harin kasuwar Goronyo a Jihar Sakkwato.
Yayin harin dai na ranar Lahadi a kasuwar wacce take ci mako-mako, akalla mutum 49 ne aka bindige a wani hari da suka bayyana da na ramuwar gayya.
- An yi garkuwa da masunta 13 a kan hanyar zuwa kamun kifi
- Najeriya a Yau: Wane tsarin zabe ya fi dacewa a Najeriya?
Daya daga cikin jagororin ’yan bindigar, wanda yake da kusanci da Kachallah Turji da Halilu Sububu, kasurguman ’yan bindiga a yankin, wato Shehu Rekeb, ya ce sun kai harin ne saboda rama kisan da aka yi wa Fulanin da ‘ba su ji ba, ba su gani ba’ a yankin.
Aminiya ta rawaito cewa kimanin mahara 100 ne a kan babura suka yi wa kasuwar kawanya sannan suka bude wa ’yan kasuwa da masu sayayya wuta, har suka kashe 49 daga cikinsu.
Ya ce, “Mun ji ana kiran maharan Goronyo da ’yan ta’adda, amma ba su ba ne. Shugaba Buhari ne muka ji yana kiransu da haka.
“Mutane Goronyo sun kashe jama’a da dama, su ma dole a kashe su,” inji Shehu Rekeb.
Da yake kawo misali da kisan wasu Fulani Musulmai lokacin da suke sallah a Unguwar Lalle, Shehu ya ce, “Lokacin da suka kashe Fulani ba mu ji Shugaban Kasa ya ce uffan ba, sai yanzu zai yi magana?”