✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa muka bude layin waya a Katsina —Masari

Abun da ya sa aka bude layukan sadarwa a kananan hukumomi 17 bayan wata uku da rufewa

Wata uku bayan rufe layukan sadarwa a wasu kananan hukumominta 17, Gwamnatin Jihar Katsina ta da bude hanyoyin sadarwar a yankunan.

A watan Satumba ne dai Gwamnatin Jihar ta sanar ta rufe layukan sadarwar a wani mataki da ta dauka da nufin karya lagon ’yan bindiga.

Sauran matakan sun hada da rufe wasu kasuwannin dabbobi, hana fataucin dabbobi, da kuma takaita zirga-zirgar ababen hawa da sayar da man fetur a sassan jihar.

A ranar Alhamis, 9 ga watan Disamba, 2021 gwamnatin wadda ta dauki matakan bayan makwabciyarta, Jihar Zamafara, ya sanar da bude layukan wayan a kananan hukumomin.

Mashawarcin Gwamna Aminu Bello Masari a kan Harkokin Tsaro, Ibrahim Muhammad Katsina, ya ce gwamnatin ta yi hakan ne bayan lura da ta yi cewa an samu saukin ayyukan ta’addanci a jihar da kuma hidimar masu ba wa ’yan ta’addan wasu bayanai.

Ya bayana cewa dalilin gwamnatin na rafe layukan sadarwa shi ne daukar matsayin matakin wucin gadi da nufin dakile ayyukan ta’addanci da masu taimaka wa ’yan ta’adda a fadin jihar, musamman a tsakanin wadannan hukumomin 17 da ’yan bindiga ke yawan yin garuwa da mutane tare da kisan gillla.

Sai dai hadimin na Gwamna Masari ya kara yin kira ga jama’a da su ci gaba da ba gwamnati goyon baya domin ganin an kawo karshen matsalar tsaro a fadin jihar da kasa baki daya.