✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa har yanzu ba mu kubutar da fasinjojin jirgin kasa ba – Buhari

Sai dai ya ce gwamnati na matukar kokari wajen ganin ta kubutar da su

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce amfani da wadanda harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya shafa a matsayin firsunoni da ’yan bindiga ke yi na daya daga cikin abin da ke ba su wahala a wajen kubutar da su.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu al’ummar Babban Birnin Tarayya Abuja da suka je masa gaisuwar Sallah a fadar gwamnati a ranar Litinin.

Idan za a iya tunawa, a ranar 28 ga watan Maris ce yan bindiga suka kai wa jirgin kasan hari, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum tara tare da raunata wasu da dama, da ma yin garkuwa da wasu fasinjojin.

Buhari ya bayyana cewa gwamnati za ta yi amfani da duk wani karfin iko da dama da ke da ita domin ceto wadanda da ke hannun ’yan bindagar.

Ya ba wa hukumomin tsaro da Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta Kasa (NRC), da a koda yaushe su kasance suna samar da bayanai ga iyalan wadanda harin ya shafa.

“Yayin da muke bikin wannan Sallah da ’yan uwa da abokan arziki, na san cewa da yawa a cikin ’yan Najeriya na cikin yanayi na tsoro da fargaba sabado mutane da dama na hannun ’yan bindinga, ciki har da wandanda aka yi garkuwa da su a harin da aka kai na jirgin kasa,” inji Buhari.

Shugaban ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance masu aiki da hukumomin tsaro ta hanyar ba su bayanai kan mabiyar ’yan ta’adda wanda zai taimaka wa yakin da suke yi.