✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa ake sace dalibai a makarantu a Arewa

Matsalar ta rage sha’awar tura yara makaranta tare da illata ilimi a Arewa

Wani kwararre a kan shugabanci, Dokta ya ce abin da ya sa ’yan bindiga suka yawaita garkuwa da dalibai a makarantu shi ne zakuwarsu ’yan bindigar sun su fara tattaunawa da gwamnati.

Dokta Ahmed wanda malamain jami’a ne ya ce, “Lamarin ’yan bindigar ya kai yadda suke ganin sai gwamnati na tattaunawa da su za su ci riba.

“Sun ga abin yadda lokacin da aka sace ’Yan Matan Chibok abin ya dauki hankalin duniya. Shi ya sa suke ganin ba za su samu irin waccan kulawar ba, sai idan sun yi garkuwa da dalibai daga makarantu; da haka ne za su fara hulda da gwamnati kai tsaye.”

Dokta Ahmed, wanda malami ne a jami’ar Nile ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindiga sun lura cewa duk lokacin da suka yi garkuwa da  wani, da mutanen gari suke tattaunawa ba, kuma ba lallai ne gwamnati ta mayar da hankali a kai ba.

“Yawancin wadanda ake garkuwa da su ana biyan kudin fansar da masu garkuwar suka bukata, amma ba ’yan ta’addar sun fi don su samu shuhura.”

Malamin ya kuma ce raunin tsaro a makarantu ya sa suke samun saukin kutsawa su kwashi mutane masu yawa a lokaci daya, sannan su yi amfani da daliban a matsayin kariya daga harin sojoji.

“Shi ya sa suke barazanar cewa idan har aka kai musu hari to za su kashe mutanen da ke hannunsu.

“Ka ga idan mutanen da ke hannun nasu na da yawa, to da wuya a kai musu hari saboda gwamnati ba za ta so a yi asarar rayuka da yawa ba,” inji shi.

Ya ce harin da ake kai wa makarantu ya jefa kasar cikin tsaka mai wuya tare da illata harkar ilimi a Arewacin Najeriya; Mutane da dama ba za su tura ’ya’yansu makaranta ba, sannan za a rufe makarantu da yawa.

“Hakan zai haifar da gibi tsakanin ’ya’yan talakawa da ’ya’yan masu kudi ta bangaren samun ilimi da ingancin ilimin tare da barazanar karuwar talauci.

“Matsalar ta rage sha’awar tura yara makaranta a Arewa, kuma duk abin da ya illata ilimi na kawo koma-bayan cigaba da arziki da tsaron kasa,  saboda yiwuwar marasa ilimi na shiga aikata miyagun laifuka,” inji shi.