Dan wasan Barcelona Lionel Messi, ya ce zai ci gaba da zama a kungiyar saboda ba zai iya biyan kudin da kungiyar ta yanke a kansa na Yuro miliyan 700 ba.
Messi ya kasance dan wasan da gungiyoyi da dama suke nema amma dalilin sharadin yarjejeniyar da ya kulla da Barcelona, babu kungiyar kwallon kafar da za ta iya biyan wadannan makudan kudade.
Messi ya ce “abin da ba zai yi wu ba ne” ga kowace kungiya ta biya wadannan kudade.
Idan kuma ba haka ba sai dai dan wasan ya maka kungiyar gaban kuliya.
Dan wasan ya zabi ya fice daga Barcelona ba tare da biyan ko sisi ba amma kungiyar ta bayyana cewa har yanzu akwai yarjejeniyar biyan Yuro miliyan 700 kafin ya bar ta a kakar wasa ta bana.
“Ina da tabbacin cewa ina da damar da zan bar Barcelona ba tare da an biya ko kwabo ba.
“Shugaban Kungiyar ta Barcelon ya ce a karshen kakar wasa ta bara zan iya yanke shawarar tafiya ko in zauna.
“Sai daga baya kuma suka ce ya kamata in sanar da su tun ran 10 ga watan Yunin bana, wanda lokacin ne kakar wasa ta bana za ta kare, sai dai kuma annobar coronavirus ta tilasta tsai da wasanni gaba daya na tsawon lokaci.
“Wannan shi ne dalilina na ci gaba da zama a kungiyar. A yanzu zan ci gaba da zama saboda Shugaban kungiyar ya ce ko dai in zauna ko na biya Yuro miliyan 700, wanda hakan ba abune mai yiwuwa ba”, inji shi.