A yau Lahadi, 7 ga watan Maris, za a yi fiti-na-fito tsakanin kungiyoyin Manchester City da makociyarta Manchester United a filin wasa na Etihad.
Wasan wanda shi ne na 27 a jerin rukunin wasannin Firimiyar Ingila ta bana wacce aka fara a watan Satumba, zai gudana ne da misalin karfe 5.30 na Yammaci a agogon Najeriya.
- Garkuwa da dalibai: Mafarautan Zamfara na neman a basu gadin marantun kwana
- Dalilin da zai sa mu rika amfani da kayan lambu a abincinmu na yau da kullum
Ana hasashen wasan zai dauki hankali a yayin da kungiyar Manchester City ke jan ragamar a teburin Firimiyar inda ta ke da maki 65 kuma ta yi wasanni 21 a jere tana samun nasara a kowanne.
Manchester City ta goge tarihin da kungiyar Arsenal ta kafa na jera wasanni 19 tana samun nasara ba tare da wata abokiyar karawarta ta riga ta jefa kwallo ba.
A yanzu Manchester United tana da maki 51 wanda ya bata damar kasancewa ta uku a teburin Firimiyar bayan Leicester City da take ta biyu da maki 54 a wasanni 28 da ta buga.
Wannan ita ce haduwa ta takwas tsakanin mai horas da ‘yan wasan Manchester City wato Pep Guardiola da kuma Ole Gunnar Solskjær na Manchester United, inda kowannensu yake da nasara uku-uku da kunnen doki daya.
Tarihi ya nuna cewa Manchester United ta yi nasara a wasanni 76 a cikin 184 da suka fafata inda ita kuma Manchester City take da nasarori 55 sai kuma wasanni 53 da suka tashi canjaras.
Ana tsammanin gidajen kallon kwallo musamman a Najeriya za su cika makil don ganin yadda wasan na yau zai kaya, inda magoya bayan kowace kungiya ke fatan samun nasara.