✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da nake fata daga shugabannin APC na kasa — Yari

Ba ni da wani matsayi na kashin kaina da ya wuce matsayin jam’iyya a hukumance.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar, yana daya daga cikin ’yan siyasar da suke nuna sha’awar tsayawa takarar Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa.

Sai dai akwai dimbin kalubale a gabansa da suka hada da rikcin cikin-gida da zarge-zargen almundahana da kudin jiharsa.

Amma a tattaunarwarsa da Aminiya ya kawar da wannan fargaba:

Ka fara taka rawa a siyasa lokacin kana kasa da shekara 30, yanzu, ina kuka tsaya game da yekuwar tsoma matasa a harkokin mulki?

Daya daga cikin manyan abubuwan da suka cancanci mutum don neman matsayin shugaban jam’iyya ta kasa shi ne gogewa da kwarewa.

Saboda haka a matsayina na wanda ya yi sa’a ya fara samun irin wannan kwarewa ina da shekara 30, ina goyon bayan tsoma hannun matasa a siyasa.

A baya mun fara hada kan siyasa ce kafin mu fara neman mukami. Lokacin ina kasa da shekara 30.

Ala kulli halin da yawa daga cikin gwamnonin wancan lokaci (1999) sun kasance masu shekara 30 ne, saboda haka ba ainihin shekaru suke da muhimmanci ba, amma abin da za ka iya kawowa.

Akwai bayanan da suke cewa kana son tsayawa takarar Shugaban APC na Kasa, ba ka tunanin jagorantar jam’iyya zuwa ga babban zabe ya kunshi manyan kalubale masu nauyi fiye da kasancewa saurayi dan siyasa mai sa’a?

A shekarar 2003, na zama Sakataren Jam’iyya a jihata, ni ne Darakta-Janar na yakin neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da na yakin neman zaben Gwamna Yerima da na kowane mutum da yake takara a rusasshiyar Jam’iyyar ANPP.

SAURARI: ‘Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Alhakin Al’umma Ne’

Mun lashe kujerun Majalisar Dokoki ta Jiha da Majalisar Dokoki ta Kasa duka kuma mun ci kujerar Gwamna. A 2004, na zama Shugaban Jam’iyya a jiha kuma labarin ci gabanmu ya ci gaba.

Duk da cewa akwai kiraye-kiraye masu karfi daga mutane na in fito takarar Gwamna in gaji Gwamna Ahmad Sani, akwai wani dalili na hankali da ya sa ba a yi haka ba, domin na fahimci hangen nesan Gwamnan cewa tunda kusan mun fito daga karamar hukuma daya ce, shi dan Bakura ne ni dan Talata Mafara, yana da kyau tikitin takarar ya ci gaba da kasancewa a wannan tsari.

Idan za ku tuna, an samar da Bakura ne daga Karamar Hukumar Talata Mafara, saboda haka asali daga karamar hukuma daya muke.

Gwamnan a wancan lokaci ya ce a’a, bari mu dauke ta zuwa wani yankin domin mu samu damar sayensu, ta yadda za ka zama Mataimakin Gwamna.

Akwai rashin fahimta don haka na yanke shawarar ba zan nemi Mataimakin Gwamna ba, kuma na zo Majalisar Wakilai ne bayan na gama wa’adina a matsayin shugaban jam’iyya.

Na kasance a Majalisar Wakilai lokacin da Gwamna Aliyu Shinkafi ya sauya sheka zuwa PDP mu muna cikin ANPP. Jam’iyyar PDP na da komai, ga Shugaba Goodluck Jonathan ga kudin mai da ikon tarayya, amma Allah Ya kaddara zan zama Gwamnan Jihar Zamfara a 2011.

Na zama Gwamna sannan na shiga tsarin hadewa don kafa APC wanda a lokacin muna da gwamnoni 11, ciki har da daya daga APGA.

A haka muka fara aikin hadewa. Mun so zama masu ci gaba ta yadda muke son kawo duk dan adawa a cikin jirgin.

Gwamnan Ondo dan Jam’iyyar Labour ne, Anambra APGA, amma Anambra da Ondo sun koma PDP a karshe sai muka ci gaba da zama 11.

A nan muka fara wannan gwagwarmaya har zuwa 2013 lokacin da PDP ta gudanar da taronta kuma muka sa sabuwar PDP ta bi mu tare da jihohinta kamar Kwara da Kano da Sakkwato muka zama 14.

Mun fara wannan tsarin hadewar kuma a zaben 2015, muka lashe dukkan kujerun jiha a Majalisar Dokoki ta Kasa sannan jam’iyyarmu ta APC ta lashe Shugaban Kasa.

Wannan shi ne inda muke a yau kuma a lokaci guda a shekarar 2015, gwamnoni abokan aikina gaba daya suka zabe ni in zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF).

Idan ka duba abin damuka yi a baya da abin da yake kasa a yanzu, batun nauyin shugabanci ba zai kasance min wani aiki mai wahala ba domin na san shi, kuma na san maballan da suka dace in matsa don hada kan mutane da cin nasara a zabe.

Ana fadin abubuwa game da kai, kamar zargin da wani sanannen gidan jarida na Intanet ya yi cewa an kama ka da Zinare na Naira biliyan 8 a filin jirgin sama na Kotoka a kasar Ghana. Me za ka ce?

Yada shirme yana iya sanya wawa a cikin babbar matsala, yayin da wanda aka yi wa batanci ya yanke shawarar zuwa kotu.

Ban taba sanin kowa a wannan wuri ba, kuma haka ni ma nake ta jin jita-jitar, ban taba samun irin wannan zinare ba.

Wannan zargi ne kawai, ba shi da wani tushe.

Wadansu mutane suna iya kirkirar karya, amma a karshe gaskiya za ta yi halinta.

Akwai sauran abubuwa da yawa da suka fada wadanda kagaggun karairayi ne da nufin bata min suna, amma ba za su yi nasara ba.

Sun yada jita-jita cewa na samu kudi daga Kulob din Landan da Paris, kaza-kaza, cewa na saci dukiyar jihar kuma na yi wannan da wancan, amma na kalubalanci kowa ko dai a cikin Kungiyar Gwamnoni ko a jihar ya kawo shaidar hakan.

A matsayina na Gwamna, mene ne aikina? Ya kasance don amfani da albarkatu da kashe kudi domin amfanin mutanena, wannan ne aikin da aka ba ni, daukar kasafin kudi da tsaretsare zuwa Majalisar Dokoki da zartar da doka da aiwatar da ayyuka.

Saboda haka, idan ba da kwangila don ayyukan ci gaba yana nufin cewa na kashe kudi a kan kwangila don samun kudi, bari Gwamnan yanzu ya ba da karin kwangila kuma ya samu kudin.

Akwai abubuwa masu sauki, kuma masu saukin fahimta wadanda wadansu masu barna suke kokarin fassarawa da gangan.

Misali yanzu muna da kwantaragin hanyoyi na miliyoyin Naira daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano, wanda aka fara sashi zuwa wasu bangarori.

Yanzu, an bayar da duk abin da aka shimfida gaba daya amma shin suna cewa Shugaba Buhari ya bayar da kwangilar ce don neman kudi?

Ko kuwa kuna kokarin fadin cewa duk ayyukan da Gwamnatin Tarayya take aiwatarwa, Buhari yana ba da su ne saboda yana son samun kudi?

Yanayi ne mara kyau sosai yin karya, wannan ba daidai ba ne.

Shin za ka iya kawar da fargabar magoya bayanka game da karar da EFCC take yi a kanka?

Babu wani abin damuwa. Babu abin damuwa. Abin da ake fada yanzu shi ne akwai wata kungiyar ’yan daba a yankin Arewa maso Yamma ta hanyar mutanen da suke sha’awar mukami na biyu, wannan ne ya sa Yari ya zama dole a kawar da shi ta kowace hanya.

Shugaban Riko na Kasa na APC ya bayyana Gwamnan yanzu da ya sauya sheka cewa shi ne jagoran jam’iyyar a Jihar Zamfara, me za ka ce game da haka?

Ba ni da abin cewa da yawa. Duk abin da nake ba su shawara su yi, duk abin da na roke su, shi ne a duk abin da suke son yi, to su bi tsarin mulkin jam’iyya su yi aiki da shi.

Su kalli kundin tsarin mulkin da kyau su yi jagoranci daga can.

Ba na takarar kowane shugabanci, mutane ne suka sa na zama shugabansu kuma za su ci gaba da kirana a matsayin shugaba muddin ina raye, ba batun APC ba ne, suna kirana shugaba.

Lokacin da nake gwamna ban taba kiran kaina shugaba ba. Ko a matsayin Gwamna mai ci, akwai wani da nake magana da shi a matsayin shugaba kuma ya sani, ina kiransa Jagora.

Jagora ne, ina kiransa, duk lokacin da ya kasance, nakan kira shi shugaba.

Duk lokacin da na gabatar da jawabi ga jama’a, nakan yi masa jawabi a matsayin jagora.

Ban taba yin maganaa kaina a matsayin jagora ba, Na yi Gwamna, wannan shi ne abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba ni kuma wannan shi ne abin da Allah Ya yanke shawarar yi.

Yaya za ka tantance damar da APC za ta samu a shekarar 2023 bisa la’akari da alkawarin da ta yi a shekarar 2015, wadanda ga alama ta gaza a kan tsaro da yaki da rashawa da inganta tattalin arziki?

Hakazalika, akwai batutuwa da yawa a bayan damar APC a 2023 ko akasin haka.

Da yawa ya dogara ga yadda muke yin lissafinmu, da yawa ya dogara ga inda muka fitar da shugabanci, wanda duk irin wadancan abubuwa gaskiya ne da ya kamata mu yi la’akari da su.

Abin da kawai zan ce shi ne idan ka kalli hadakarmu, daga Arewa da shiyyoyin da muka dauka don tafiya tare, Kudu maso Yamma musamman, idan ka dube ta sosai kuma ka kalli abin da ya faru, daga can ne za mu iya daukar mataki mu ce daidai.

Wannan shi ne abin da ya kamata mu yi a matsayinmu na jam’iyya ko kuma wannan shi ne abin da bai kamata mu yi ba a matsayinmu na jam’iyya.

Sannan a hankali mu kalli wasu kura-kurai da muka yi a shekara shida kuma ga yadda za mu iya matsawa da sauri a matsayin jam’iyya da kuma a matsayin gwamnati don ganin yadda za mu iya rufe kusan kashi 30 zuwa 40 cikin 100.

Daga nan sai mu shawo kan mutane kuma mu tambaye su, mun yi alkawarin abubuwa da yawa da za mu yi ba za mu cuce ku ba saboda mun samu abubuwa da yawa wadanda ba su saiti.

Dangane da batun tattalin arziki, muna sa ran samun farashin mai a Dala 100 zuwa 120 kan kowace ganga amma ya sauka zuwa Dala 27 kan kowace ganga kuma yanzu bai wuce Dala 70 ba.

Akwai abubuwa da yawa da za mu tattauna akwai rashin tsaro da rashin aikin yi da sauransu.

Akwai abubuwa da yawa da ya kamata mu duba da muke yin iya kokarinmu.

Akwai abubuwa da yawa da za a duba cikin tsarin, musamman tsakanin yanzu zuwa badi.

Mece ce amsarka ga yekuwar zakudawa da mulki zuwa Kudu?

To, ba ni da wani matsayi na kashin kaina da ya wuce matsayin jam’iyya a hukumance.

Idan manyan shugabannin APC sun yi alkawarin cewa mulki ya koma kowane wuri, ya kamata mu girmama shi.

Ba za mu samu dalili ba don tilastawa amma ya kamata mu kalli wannan da sauran abubuwan da kyau domin APC ta ci gaba da samun nasara a gaba.

SAURARI: ‘Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Alhakin Al’umma Ne’