Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Zariya, inda suka tattauna abubuwan da suka shafi siyasar Najeriya.
Farfesan Ango Abdullahi ya shaida wa Aminiya a ranar Litinin cewa tambayar farko da tsohon shugaban ya yi mishi ita ce, “Wai shin kasar nan ta shirya samun jagoranci nagari a zabe mai zuwa kuwa?”
- ’Yan sanda sun gano idanun da aka kwakule wa yaro a Bauchi
- ‘Yunwa ta kashe mutum 23 a sansanin ’yan gudun hijira da ke Katsina’
Ango Abdullahi wanda ya ce ziyarar Obasanjo ta zumunci ce, kamar yadda suka saba kai wa juna, ya ce sun tattauna sosai a kan harkar siyasa da kuma makomar Najeriya a zaben 2023 da ke tafe.
Ya ce ra’ayinsa da na Obasanjo sun zo kusan daya, “Cewa dukkan manyan ’yan takarar jam’iyyu biyun nan da aka tsayar masu neman kujerar mulkin kasar nan ba su da cancantar fitar da kasar daga halin ha’ula’in da take ciki a halin yanzu.
“Wannan shi ne ra’ayina, ina nan kuma a kansa har yanzu.” in ji shi.
Ya bayyana cewa wannan ra’ayi nasa ne na kashin kansa, saboda duka ’yan takarar biyu ya san su sosai, har ma ya yi aiki da daya daga cikinsu a kusa sosai.
Ya ci gaba da cewa idan manyan jam’iyyun suka gagara yin abin da ya dace, jama’a na da sauran zabi, tun da akwai wasu ’yan takara har guda 15 a sauran jam’iyyu.
Ddangane da matsayar Kungiyar Dattawan Arewa a kan zaben da ke tafe, Tsohon Shugaban na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya ce Kungiyar ba ta da wata matsaya da ta wuce samun nagartaccen shugaban da zai fitar da jama’a daga halin ha’ula’in da suke ciki.
Ya kara da cewa, kungiyar ba ta damu da bangaren da irin wannan jagoranci zai fito ba, indai har za a samu zakakuri, masanin shugabanci.
Duk da haka, ya yi fatar ganin an zakulo irin wannan shugaban daga yankin Arewacin Najeriya.