Fim sin Sanda mai dogon zango, zango na biyu shiri ne da Adam Abdullahi wanda aka fi sani da Abale ko Daddy Hikima ya shirya.
Matashin wanda a yanzu ke jan zarensa a masana’antar Kannywood ya bayyana wa Aminiya cewa an shirya fim din ne domin ankarar da jama’a halayen wadansu mutane da kan yi amfani da matsayinsu ko kafar sada zumunta su rika bata tarbiyyar ’ya’ya mata:
Wane sako ne fim din Sanda zango na biyu yake dauke da shi a takaice?
An fara shirin ne a kan idan ka ga mutum yana abu marar kyau ko daba ko shaye-shaye in kai mahaifi ne kada ka tsine masa saboda ba ka san wa za ka haifa ba.
Idan ka la’anci wani, to ba ka san yadda Allah zai shirye shi ba. Idan yana da kyakkyawar alaka a tsakaninsa da iyayensa ko me yake yi sai ka ga yana ta samun nasara.
Daya daga cikin sakon da ake nunawa shi ne karfin soyayyar iyaye musamman soyayyar mahaifiya.
Sanda wani irin mutum ne mai zuciya saboda kuma ga shi saboda yana da zafin son mahaifiyarsa fiye da komai ko me yake yi ko aka bata masa saboda ita sai ya hakura.
Amma a zango na farko mahaifiyar Sanda ta sha fama da ciwo, amma ya ki zuwa duk da cewa kanwarsa ta kira shi…
Abin da ya faru akwai takardar sayen magungunanta da kudin da za a saya duk a cikin karamar jakar ajiye kudi kuma akwai takardar magani da likita ya rubuta za a saya na ciwon hawan jini da ciwon sukari kuma takardar tana cikin jakar nan da kudin sayen maganin gaba daya.
Ka ga ba zai iya karbo maganin ba, dole sai da wannan takardar dole sai ya koma ya dauko takardar a gidan.
Ka ga bayan an ga mahaifyar Sanda ta rasu, a zango na biyu ta dawo, dama ba mutuwa ta yi ba.
Abin da ya faru ana so a yi wani abu ne da yawanci mutane suke samu kamar bangaren kiwon lafiya idan har aka zo kamar karin ruwa ko karin ruwa wani abu ne da yake amfani da zuciya.
Sai muka nuna illar idan yanzu misali ita mahaifiyar Sanda a gida ai an zo an kara mata ruwa to lokacin da ake kara mata ruwa to akwai wata kanwar Sanda aka yi rikici da ita da ma’aikaciyar kiwon lafiya kawai sai ta kara wa ruwan gudu.
To, wannan ruwan da ta kara wa gudu shi ya janyo wani abu da ake cewa Hyperbolomic shock (Bugawar zuciya).
Zuciya tana kai wani mataki idan ruwa aka sako shi yake shigowa ba yadda ya dace ba, to zai iya sanya zuciyar ta daina bugawa.
Shi ne sai ta suma, daga baya labarin ya dawo da ita.
Shin akwai korafe-korafen da ka samu a kan zango na farko da aka gyara a zango na biyu?
Akwai korafi, masu kallo ba sa son wannan gida da na je na zauna na tsohuwar budurwata.
Sannan akwai korafin ta yaya ma za a ce mahaifiyarsa ta mutu saboda idan ba ita ba, lallai ba za a iya sarrafa Sanda ba.
To dalilin haka ne muka yi duk abin da ya kamata domin jin dadin masu kallo saboda dama ai don su ake yi.
Duk abin da bai yi musu ba, to dole ka canja, shi ne dalilin da ya sa da za mu yi rubutun zango na biyu muka kalli rubutun daga farkon fitowar na daya har zuwa karshensa muka yi amfani da jawaban muka gyara yadda za a yi domin ya kayatar.
Sannan a zango na biyu mun yi karin jarumai sababbi domin shirin ya kara armashi.
Akwai jarumai fitattu irin su Tijjani Faraga da Al-Amin Buhari da Garzali Miko da Ruky Alim da Isa Ferozkhan da sauran jarumai da dama da aka karo. Jarumai dai sun kai akalla 50.
Kana ganin fim din ya samu karbuwa wajen mutane?
Ya samu karbuwa kwarai da gaske saboda akwai darussa da dama.
Idan zan bude maka labarin ne kamar wani abu da yake faruwa da ’yan mata a cikin gari, sai ka ga budurwa tana soyayya da wani saurayi saboda yadda waya ta yawaita.
Sai ya kasance saurayin ya yi amfani da wannan so da take masa ya yi mata bidiyo na tsiraicinta ya rika tura mata.
To fa duk lokacin da yake bukatarta dole ta fito ta zo. Irin wadannan abubuwa da samari ke yi wa ’yan mata muka kara bude wa mutane ko mata ido cewa su daina yin haka saboda saba wa addini da al’adunmu.
Don haka irin wadannan abubuwa kuskure ne da mata suke yi, a ce su yarda da maza irin wannan, har a samu matsala.
A zango na farko Sanda na karatu a jami’a ko ya samu kammala karatun?
Bai kammala jami’a ba sakamakon yana cikin jami’ar ya yi kisan kai aka kai shi kurkuku.
Ko yana fitowa ya ci gaba?
Ya fito daga kurkuku ya ci gaba da karatu ya tafi soja.
Kana da sako ga masoya da masu son fim din Sanda?
To sakona a kowane lokaci a kasance da tasharmu ta YouTube Daddy Hikima TV, duk wasu shirye-shirye kayatattu za su gan su a cikin wannan tasha.
Yadda muka yi wannan fim din zango na 2, in Allah Ya yarda za a samu abin da zai amfanar.
Sannan matasa a ci gaba da hakuri, rayuwa tana cike da kalubale masu yawan gaske, amma idan aka yi hakuri sai a samu nasara.
Me ya sa ba ka nuna fina-finanka a sinima?
Gaskiya abin da ya sa ba na son nuna fina-finaina a sinimomi shi ne ka ga na farko masoyanmu da dama ’yan yankunan da babu sinima ne, wadansu kuma ba su da ra’ayin kallo a sinima.
Za ka ga misali a garina Kano da sauran garuruwa matasa masoyanmu yawanci ’yan A Daidaita Sahu ne, to ina alfahari da masu A Daidaita Sahu ciki da wajen Najeriya kuma ka ga suna aiki daga safe har dare, don haka ba su da lokacin zuwa sinima kallo.
To amma lokacin da nake saka fim dina da daddare karfe 8:00 na san sun tashi daga aiki.
Idan na ce na kai sinima ba za su iya samun damar shiga ba. Wannan shi ya sa, ba wai ba na son kudin ba ne.